Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi: Ba a taba ganin wanda ba shi da kunya kamar Peter Navarro ba
2019-10-21 17:18:17        cri
A ranar 21 ga wata, Babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin CMG ya buga sharhi mai taken "Ba a taba ganin wanda bashi da kunya kamar Peter Navarro ba".

Sharhin ya nuna cewa Peter Navarro, babban mai bada shawara ga shugaban kasar Amurka ta fuskar tattalin arziki ya kago wani kwararre kan batun kasar Sin, sa'an nan ya sayar da littattafansa a ko ina, inda ya zargi kasar Sin da miyagun kalamai, lamarin da yasa aka sake fahimtar rashin kunyar da masu tsattsauran ra'ayi na kasar Amurka ke dashi.

Abin da ya wuce zaton mutane shine, bayan da aka tona karyar Peter Navarro, mutumin nan ba ya jin kunya ko kadan, a maimakon hakan, ya ce wasa ne kawai ya tsara sunan Ron Vara. Abin da ya fusata mutane sosai, har ma wani kwararre ya ce: "Na taba ganin wasu marasa kunya, amma ban taba ganin wanda ya rasa kunya kamar Peter Navarro ba."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China