Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Masana daga kasashen Uganda da DR Congo sun gana don kimanta ci gaban da aka samu a yaki da Ebola
2019-10-21 20:35:21        cri
A yau ne ministocin lafiya daga kasashen Uganda da Jamhuriyar demokiradiyar Congo da wakilan WHO da AU ke ganawa a garin Goma dake gabashin DRC, don kimanta ci gaban da aka samu da shawarwarin da aka bayar a taron kasashen da ya gabata, da nufin kawo karshen kwayar cutar Ebola dake kisa.

A watan Yuli ne, babban darektan hukumar lafiya ta duniya(WHO) Tedros Adhanom ya ayyana barkewar kwayar cutar, wadda ta halaka rayukan mutane sama da 2,000 a jamhuroiyar demokiradiyar Congo, a matsayin matsalar lafiyar jama'a dake jawo hankalin kasa da kasa na gaggawa.

A nata bangaren kungiyar tarayyar AU, ita ma a watan Yulin, ta ba da umarnin tura wata tawagar yaki da cutar ta Ebola zuwa kasar DRC.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China