Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An sanya tsohon garin Liangzhu cikin jerin sunayen muhimman al'adun gargajiyar duniya
2019-11-01 16:38:18        cri


Yau za mu yi muku bayani game da tsohon garin Liangzhu na birnin Hangzhou na lardin Zhejiang dake kudu maso gabashin kasar Sin, wanda aka shigar da shi cikin jerin sunayen muhimman wurare na gargajiya na duniya a watan Yulin bana.

A ranar 6 ga watan Yulin, agogon Baku, fadar mulkin jamhuriyar kasar Azerbaijan, an zartas da wani kuduri a yayin taron kwamitin kula da muhimman al'adun gargajiyar duniya na 43 na hukumar kula da harkokin ilmi da kimiyya da al'adu ta MDD wato UNESCO, inda aka sanya tsohon garin Liangzhu na kasar Sin a cikin jerin sunayen wuraren gargajiya masu muhimmanci na duniya bisa ma'aunin sashe na 3 da na 4 da kwamitin kula da muhimman al'adun gargajiyar duniya ya tsara, daga nan sai adadin muhimman al'adun gargajiyar kasar Sin da aka shigo da su cikin jerin sunayen duniya ya kai 55.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China