Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An gudanar da bikin CIIE karo na biyu a kasar Sin
2019-11-11 14:01:30        cri

 

Daga ranar 5 zuwa 10 ga wata ne, aka gudanar da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyu, wato CIIE a takaice, a birnin Shanghai na kasar Sin. Bikin na wannan karo ya samu halartar kamfanoni sama da 3000 daga kasashe ko yankuna fiye da 150, wadanda suka fito daga nahiyoyi biyar. To ko mene ne CIIE? Me aka yi a wajen bikin? Mene ne ma'anar bikin kuma?


 
Me ka sani game da CIIE?

CIIE, wato China International Import Expo a Turance, biki ne da ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta shirya tare da hadin gwiwar hukumar birnin Shanghai, a wani kokari na bayyana goyon baya ga 'yancin ciniki da kuma dunkulewar tattalin arzikin duniya baki daya.

Bikin ya kasance irinsa na farko a duniya da ke baje kolin kayayyakin da wata kasa ke shigowa daga kasa da kasa, wanda kuma ya kasance wani babban matakin da aka dauka a tarihin cinikayyar kasa da kasa, haka kuma muhimmin mataki ne da kasar Sin ta dauka, na kara bude kasuwarta ga kasashen duniya.
A bara ne aka kaddamar da bikin a karo na farko, kuma a kan gudanar da shi daga ranar 5 zuwa 10 ga watan Nuwamba a birnin Shanghai da ke gabashin kasar ta Sin.


 
CIIE, mun dawo!
Daga cikin kamfanonin kasa da kasa sama da 3000 da suka shiga bikin na wannan shekara, akwai kamfanoni 206 da suka fito daga kasashen Afirka daban daban, ciki kuwa har da kamfanoni na kasashen Nijeriya da Nijer da Ghana da sauransu.
Madam Temitope Akintunde, mataimakiyar shugaban sashen kula da hulda da kasa da kasa da na al'umma, karkashin majalisar masana'antu da kasuwanci ta Lagos, ta jagoranci tawagar 'yan kasuwa mambobin majalisar zuwa wajen bikin na wannan shekara, kuma ta yi farin ciki da cewa, "Mun amfana da abubuwa da yawa a bikin na farkon, shi ya sa muka dawo."
Malamar ta kara da cewa, 'yan kasuwa mambobin majalisar da suka halarci bikin na bara, yanzu haka sun sha yin ciniki da takwarorinsu na kasar Sin, ko shakka babu bikin CIIE ya samar musu damammaki masu yawa, haka kuma ya bude musu kofar shiga kasuwannin kasa da kasa. A sabili da haka, bayan kammala bikin na farko, sai aka bukaci halartar bikin na wannan shekara, sabo da gaskiya sun amfana sosai.


A cewar Madam Temitope Akintunde, gaba daya akwai kamfanoni mambobin majalisar 13 da suka halarci bikin, adadin da ya kusan karuwa har sau biyu, idan an kwatanta da yadda kamfanoni 7 suka halarci bikin a bara.
Chika Agnes Nwozo daya ce daga cikin 'yan kasuwar Nijeriya da suka halarci bikin na wannan shekara karkashin tawagar majalisar, kuma tana kokarin tallata kayayyakin da ta kawo a wajen bikin kamar haka, "Kuma muna da man kadanya. Mai ne da ake shafawa a fata, yana gyara fata sosai. Yana kuma da kamshi mai dadi. Za a iya shafawa yara, har ma iyaye da kowa da kowa."


Tallan Chika ya jawo hankalin masu sayayya da ke wucewa ta rumfarta, har ma sun tsaya sun duba, wasu da suka nuna sha'awar kayanta ma sai suka yi musayar bayanan juna.
Chika Agnes Nwozo tare da mai gidanta Chimezie Nwozo na gudanar da wani kamfanin cinikin waje mai suna ۢ@ޢ a Lagos. A bikin CIIE na wannan shekara, sun kawo man kadanya, da sabulun Dudu-Osun, da tsakiya, da ma tufafin gargajiya na Nijeriya. Chika ta ce, wannan ne zuwanta na farko bikin CIIE, amma a bara mai gidanta ya taba halartar bikin na farko, karkashin jagorancin hukumar bunkasa masana'antu da kasuwanci ta Lagos.


Chimezie Nwozo, mijin Chika ya bayyana cewa, kafin halartar bikin CIIE karo na farko, suna sayar da kayayyakinsu ne zuwa kasashen Burtaniya, da Faransa, da Amurka, da dai sauran kasashen Turai, sai dai bikin CIIE ya ba su damar shigar da kayansu kasuwar kasar Sin. Ya ce, kasuwar kasar Sin tana matukar daukar hankalin al'umma, don haka, kullum suna kokarin neman shigar da kayayyakinsu cikin kasuwar, kuma tabbas bikin CIIE da aka gudanar karo na farko a bara, ya samar musu damammaki na yin kasuwanci. Ya ce,  "Da muka zo a bara, mun zo da sabbin kayayyaki ga kasuwar kasar Sin. Mun yi mamaki da muka ga Sinawa na sha'awar abun da muka kawo daga Nijeriya, kuma sun yi ta tuntubarmu bayan mun koma. Kuma muna ta hadin gwiwa da wasu tun daga wancan lokacin. Mun samu damammakin kasuwanci da dama, don haka muka dawo, domin na bana zai fi na bara armashi."


Madam Temitope Akintunde, mataimakiyar shugaban sashen kula da huldar kasa da kasa da na al'umma karkashin majalisar masana'antu da kasuwanci ta Lagos, ta bayyana cewa, tun bayan halartar bikin CIIE karo na farko, gaba daya kayayyakin da kamfanoni mambobin majalisar masana'antu da kasuwanci ta Lagos suka sayar ga kasuwannin kasar Sin sun kai kimanin dala miliyan. Ta ce, kasar Sin muhimmiyar abokiyar ciniki ce ta Nijeriya, don haka, bikin CIIE ya kasance wani muhimmin zarafi ga kamfanonin Nijeriya, wanda ya samar da wani muhimmin dandali na yin musayar ra'ayoyi, da ma hadin gwiwa a tsakanin 'yan kasuwar kasashen biyu. Malamar ta kuma jaddada cewa, kwatankwacin yawan cinikin da aka cimma, abin da ya fi muhimmanci shi ne, bikin ya kara karfafa huldar abokantaka a tsakanin sassan biyu, ta ce, "Yanzu haka ana gudanar da baje kolin kasa da kasa a Lagos. "Mu muka shirya baje kolin. Kuma yanzu haka, adadin Sinawa masu baje hajojinsu a wajen ya rubanya na bara. Don haka mutanen da suka san Nijeriya da Afrika, da suka zo don yin kasuwanci da mu ya rubanya sau 2 akan baje kolin CIIE na bara. Gaskiya bikin CIIE ya ba mu dama."
Madam Temitope Akintunde ta kuma yaba da shirya bikin CIIE da kasar Sin ta yi, wanda a ganinta mataki ne na kara shigo da kayayyaki daga ketare, da ma kara bude kasuwarta ga kasa da kasa, tana mai cewa,   "Wannan ya kasance amsa ga kariyar ciniki da wasu suke yi a duniya. Idan aka ci gaba da gudanar da shi a haka, za a samu saukin shiga kasuwar kasar Sin, kuma tattalin arzikin kasar zai ci gaba da habaka kamar yadda ya saba."


 
Dan kasuwar kasar Sin a wajen CIIE

Mr.Zhao Haoxing, wanda ya kafa dandalin hada-hadar ciniki da ake kira Zhongfeiqiao, dandalin da ke samar da hidimomin hada-hadar ciniki a tsakanin Sin da Afirka tare da horar da matasan Sin da Afirka a kan harkokin kasuwanci, ya halarci bikin CIIE na bara, kuma ya halarci bikin na wannan shekara, kuma a ganinsa, karin kamfanonin kasashen Afirka na halartar bikinAkuma karin kayayyakin kasashen Afirka na shiga kasuwar kasar Sin. Ya ce, Afirka na da maka-makan filaye da muhalli mai inganci, kuma Allah ya albarkaci kasashen nahiyar da nau'o'in kayayyaki masu inganci da suka hada da amfanin gona da kayayyakin kiwon lafiya da lu'u lu'u da damar bunkasa yawon shakatawa da dai sauransu.

Ya ce, a halin da ake ciki yanzu, kasashen Afirka na fuskantar babbar dama ta shigar da kayayyakinsu kasuwar kasar Sin, sai dai kuma akwai kalubale a sakamakon yadda 'yan kasuwar kasashen Afirka suka gaza yin nazari kan kasuwar kasar Sin da ma wayar da kan al'ummar kasar kan hajjojin da suke da su, kuma ba su kware wajen alkintawa da kuma yayata kayansu ba. Yana mai cewa, "Masu sayayya na kasar Sin ba su fahimci kayayyakin Afirka sosai ba, kuma ma'anar bikin CIIE ke nan, wato ya wayar da su cewa, ashe akwai nau'o'in hajjojin Afirka masu yawa haka. Sa'an nan, duk da cewa masu sayayya na kasar Sin ba su fahimci kayayyakin Afirka sosai ba, amma suna sha'awarsu. Da yawa daga cikin al'ummar Sinawa ba su taba zuwa kasashen Afirka ba, don haka, ba su san me ake da su a kasashen Afirka ba, amma yadda suke da sha'awa zai iya samar da babbar kasuwa ga kayayyakin Afirka."

Mr.Zhao Haoxing ya ce, a bikin na bara, ya cimma hadin gwiwa da wani kamfanin sarrafa jar barasa na kasar Afirka ta kudu, kuma da yake halartar bikin na wannan shekara, yana kokarin gano karin damammakin ciniki da 'yan kasuwar Afirka, inda ya tuntubi wasu 'yan kasuwar Afirka da suka baje kolin kayansu a wajen tare da yin musayar bayanan juna, domin gano damar yin hadin gwiwa.


 
Yaya za a amfana daga bikin CIIE?

Adamu Mohammed AbdulHamid, wakilin tarayyar Nijeriya a WTO, yana daya daga cikin bakin da aka gayyato zuwa bikin. A ganinsa, bikin zai taimaka wajen kyautata daidaiton ciniki a tsakanin Sin da Nijeriya, yana mai cewa, "Zai taimaka, saboda yanzu kamar yadda muka fadi, idan kayayyakin da mutanen Najeriya suka kawo, kuma 'yan China suna bukatarsa, kuma suka fara shigo da kayan daga Najeriya zuwa nan, ai abinda ake kira "export balance" din mu zai karu, misali kamar ridi sai a duba a gani cewa ton nawa ake kawowa daga Najeriya zuwa China. Misali ko rogo ko kuma ganyen rogo, duka wadannan kowanne yana da sunansa. Watakila a yanzu babu wadanda suke yin wannan harkar kasuwancin sosai, to amma wannan abinda aka zo aka yi sai suka ga cewa ai kamar Najeriya suna da kaza, wanda mu a nan bamu da shi da yawa, saboda haka yanzu abinda za'a yi shine sai mu hada hannu da ku, muna bukatar a samu katon kaza, ton kaza, idan suka yi wannan yarjejeniyar, shi ke nan sai su tabbatar da yanayin ingancin da ake bukata a China yayi daidai da abinda ake bada dama a shigo da shi nan, to idan suka yi hakan shi ke nan, zaki ga idan a da ana shigo da ton miliyan biyu ne ko miliyan uku, to sai ki ga tunda yanzu sun samu abokan harka a nan, sai ki ga an kara shi zuwa wajen ton miliyan 10 ko sama da haka, to kinga hakan zai nuna cewa ainihin abinda muke fitarwa zuwa waje, wato kayan dake shigowa nan ya karu ke nan, to idan kaya ya shigo abinda ake kira "foreign exchange" wato kudaden musayar kasashen waje ya kan karu ga kasa. Idan suka kawo nan suka sayar, ba a nan zasu kashe kudinsu ba, can zasu koma da kudinsu Najeriya, to kinga musayar kasashen waje ya karu."


Bikin CIIE kusan ya kasance bikin baje kolin da ake shigo da kayayyaki daga kasa da kasa irinsa na farko a duniya, wanda kuma ya kasance muhimmin mataki da kasar Sin ta dauka a fannin kara bude kofarta ga kasashen duniya. A yayin da duniya ke fuskantar matsalar kariyar ciniki, Mr. Adamu Mohammed AbdulHamid ya ce, yadda aka gudanar da bikin CIIE yana kuma da ma'ana ta musamman. "Abin da shi kan sa shugaban kasar ya fada a wajen bude taron shi ne, hannu daya ba ya daukar jinka, matakin ne ya dauka, wanda gaskiya ba a samu wata kasa da ta bude bikin baje kolin na abin take bukatar a rika shigo da su ba, sai ta shirin bikin baje kolin na abubuwan da suke da su, mutane su ga ni su rika saya. Amma sai kasar Sin ta ce a zo a shirya bikin baje kolin na abubuwan da ake shigowa da su daga wasu kasashen, saboda mutanensu a nan su ga abubuwa, su kuma san wadanne kasashe ne suke da irin wadannan kayayyaki, saboda su ma su fara harka da su, sai su rika zuwa suna sayowa, harka ce da suka nuna suna son su yi mu'amala da kasashen duniya dangane da harkar kasuwanci, suna son su bunkasa harkar kasuwancinsu." (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China