Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
An bude taron kolin kungiyar ASEAN karo na 35
2019-11-03 17:01:08        cri
Yau Lahadi, an yi bikin bude taron kolin kungiyar tarayyar kasashen dake kudu maso gabashin nahiyar Asiya karo na 35, wato ASEAN, da kuma tarukan hadin gwiwar kasashen dake gabashin nahiyar Asiya a birnin Bangkok, fadar mulkin kasar Thailand.

A yayin bikin budewar, shugaban kungiyar ASEAN, kana firaministan kasar Thailand Prayuth Chan-ocha ya bada jawabi cewa, ya kamata kasashen kungiyar ASEAN da abokan kungiyar su karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu, domin fuskantar kalubalolin dake gabansu cikin hadin gwiwa, da kuma samun dauwamammen ci gaba.

An yi taron kolin kungiyar ASEAN da taruka hadin gwiwar kasashen dake gabashin nahiyar Asiya daga ranar 2 ga wata zuwa ranar 4 ga wata a birnin Bangkok na kasar Thailand. Kuma gaba daya akwai kasashe guda 10 dake cikin kungiyar ASEAN, wadanda suka hada da kasashen Indonesia, Thailand, Singapore, Philippines da kuma Malaysia da dai sauransu. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China