Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin ta ba da gudunmawa wajen kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa
2019-11-05 15:51:55        cri
A yau Talata ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi mai taken "Bude kofa da hadin kai don kafa makoma ta bai daya" a yayin bude bikin baje kolin kasa da kasa na kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin karo na biyu a birnin Shanghai. A cikin jawabinsa, Xi Jinping ya ba da shawarwari 3 dangane da dunkulewar tattalin arzikin duniya, kuma ya sanar da cewa, a matsayinta na kasa ta biyu mafi karfin tattalin arziki a duniya, Sin za ta ci gaba da aiwatar da muhimman matakai 5 don kara bude kofa ga ketare, ta yadda kasar Sin za ta ba da gudunmawa wajen ingiza kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya, matakin da ya bayyana yadda Sin take sauke nauyin dake wuyanta a matsayinta na babbar kasa.

Sin dake da yawan al'umma fiye da biliyan 1.4, masu matsakaicin kudin shiga mafi yawa a duniya, tana ba da gudunmawa na kashi 30 cikin dari ga bunkasuwsar tattalin arzikin duniya shekaru da dama a jere, kuma yanayin ciniki a kasar ya ci gaba da kyautatuwa. Xi Jinping ya yi imani cewa, tattalin arzikin Sin na da makoma mai haske a nan gaba.

Ban da wanann kuma, Sin dake kara bude kofa ga ketare za ta samarwa sauran kasashe damammaki masu dimbin yawa, matakin da ya sa ta zama muhimmin karfi dake ingiza kafa tsarin tattalin arzikin duniya mai salon bude kofa da raya kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China