Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yarjejeniyar Sauyin Yanayi Da Tasirinta Ga Duniya
2019-11-06 19:11:07        cri

Batun janyewar kasar Amurka daga yarjejeniyar sauyin yanayi da aka cimma a birnin Paris na kasar Faransa a shekarar 2015, na cikin manyan batutuwa masu matukar daukar hankulan sassan kasa da kasa a halin yanzu, kasancewar nasarar tana iya shafar ci gaban rayuwar bil Adama baki daya.

Majalissar dinkin duniya ce dai ta dauki nauyin shirya wannan yarjejeniya, a wani mataki na hade kan kasashen duniya waje guda, domin yin aiki tare, wajen daukar matakan rage hayaki mai gurbata muhalli dake haifar da mummunan tasiri ga yanayin muhallin duniya.

Daya daga manyan kudurorinsa shi ne rage irin wannan hayaki da ke gurbata muhalli da kasashe musamman masu karfin masana'antu ke fitarwa, ta yadda ba zai dara wani mizani da aka gindaya, mai nasaba da yanayin muhallin duniya kafin juyin juya halin masana'antu da aka samu ba.

Tuni dai Amurka ta bayyana aniyarta ta ficewa daga wannan yarjejeniya nan da shekarar 2020 mai zuwa, inda har ma shugaban kasar Dornald Trump ya bayyana cewa, matakin kariya ce ga Amurkawa, duba da irin makudan kudade da kasar za ta ci gaba da kashewa idan har ta ci gaba da kasancewa a cikin wannan yarjejeniya.

Manazarta dai na ganin wannan mataki na Amurka, shi ne mafi muni da gwamnatin za ta aiwatar, wanda zai kwance alkawarin da tsohuwar gwamnatin shugaba Obama ta dauka ga duniya.

Wasu muhimman abubuwan lura dai game da wannan batu su ne:

Amurka na ikirarin cewa, ba za ta cimma wata riba daga ci gaba da kasancewarta a yarjejeniyar ba, ba kuma tare da la'akari da cewa, tana sahun gaba a jerin kasashe masu fitar da gurbatacciyar iska dake tasiri ga yanayin duniya ba.

Bayan shigar kasashe da yankunan duniya kusan 200 cikin wannan yarjejeniya, kwamitin kasa da kasa na aiwatar da ita, karkashin MDD ya yi kashedin cewa, idan har ba a aiwatar da matakan da suka wajaba ba, tasirin sauyin yanayi na iya yin mummunar barna ga rayuwar al'ummar duniya. Masana sun ma yi kashedin cewa, idan har ba a dauki mataki ba, ya zuwa shekarar 2050, yawan al'ummun duniya da za su rasa matsugunnin su sakamakon bala'u masu nasaba da sauyin yanayi, zai kai mutum miliyan 143.

Wani babban abun tsoro game da ficewar Amurka daga wannan yarjejeniya, musamman a gabar da sauran kasashen duniya, ciki hadda Sin da Faransa ke hankoron karfafa ta shi ne, mai yiwuwa hakan ya sanyaya gwiwar sauran kasashen duniya, ta yadda za su gaza cika alkawuran da suka dauka na cimma nasarar ta. Hakan zai kuma aike da wani sako ga sauran sassan duniya dake nuna cewa, Amurka ba ta damu da duk wani yunkurin kasa da kasa na kare muhalli ba.

To sai dai kuma a hannu guda, abun da za a zuba ido a gani shi ne, ko aniyar manyan kasashen duniya game da cimma muradun wannan yarjejeniya zai yi nasara? Shi ko sauran kasashen duniya za su iya cike gibin da Amurkar za ta samar?

Koma dai yaya ta kaya, babu wani bil Adama da zai iya musanta muhimmancin wannan yarjejeniya, da ma irin tasirin da za ta yi ga kyautata rayuwar al'ummar duniya ta hanyar kare muhallin da ya zamo na kowa da kowa. Duniya kuma ba za ta manta da irin gudummawar da sauran kasashen duniya masu dora muhimmanci kan yarjejeniyar ke bayawar ga rayuwar bil Adama a yau, da ma zuriyoyin da za su biyo baya ba! (Saminu Hassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China