Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Tilas ne dakarun wanzar da zaman lafiyar MDD su bi dokoki
2019-11-07 09:54:10        cri

Wakilin kasar Sin ya ce wajibi ne dakarun shirin wanzar da zaman lafiya na MDD su mutunta ka'idoji da dokokin da aka amince da su karkashin yarjejeniyar ayyukan MDD.

Da yake jawabi a lokacin taron muhawara na kwamatin sulhun MDD game da batun 'yan sandan shirin wanzar da zaman lafiya na MDD, Zhang Jun, wakilin dindindin na kasar Sin a MDD, ya nanata cewa, tilas ne kwamitin sulhun MDD ya mutunta 'yancin cin gashin kai da kasashen duniya ke da shi da kuma burin da kasashen dake karbar bakuncin jami'an shirin MDDr ke son cimmawa, gami da ba su 'yancin bayyana ra'ayoyinsu, da kasashen dake bayar da gudunmowar 'yan sandan kiyaye zaman lafiyar.

Ya ce kamata ya yi kwamitin MDDr ya fayyace komai a bayyane wanda ya dace da yanayin da ake ciki, sannan ya yi kyakkyawan amfani da jami'an 'yan sandan shirin wanzar da zaman lafiya a kasashen da suke gudanar da aikin don tabbatar da doka da oda yadda ya kamata, kuma su samar da wani ingantaccen yanayin ci gaba.

Zhang ya ce, wajibi ne a samar da wani yanayin zuba jari na dogon zango a fannin tattaunawar siyasa, da raya tattalin arziki, domin samar da dawwamamman zaman lafiya.

Haka zalika ya bukaci a kara kokarin kyautata yanayin kwarewar jami'an 'yan sandan shirin wanzar da zaman lafiyar domin su samu damar aiwatar da ayyukansu yadda ya kamata, da kuma tabbatar da tsaron lafiyar jami'an 'yan sandan shirin wanzar da zaman lafiyar.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China