Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CIIE babbar dama ce ga kamfanonin Masar
2019-11-07 13:10:10        cri

Wani masanin al'amurran kasar Sin ya ce, bikin baje kolin kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin karo na 2 (CIIE) muhimmiyar dama ce ga kamfanonin kasar Masar inda za su samu damar yin takara a kasuwannin kasar Sin.

Ahmed Sallam, tsohon kwararren masanin harkokin yada labarai a ofishin jakadancin kasar Masar a kasar Sin, ya bayyana haka a tattaunawarsa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua.

Sallam ya ce, halartar kamfanonin Masar 23 a baje kolin CIIE karo na 2, a daidai lokacin da kasar Sin ke duba yiwuwar kara shigo da kayayyaki daga waje na dala tiriliyan 10 cikin shekaru 5 masu zuwa, ana sa ran matakin zai kara bunkasa yawan kayayyakin da Masar ke shigarwa kasuwannin kasar Sin.

Ya ce kasar Sin za ta bayar da babbar dama ga masu zuba jarin waje don su samu damar shiga kasuwannin kasar Sin, kuma a samu bunkasuwar fannonin zuba jari da samun kariya.

A ranar Talata aka bude bikin baje kolin na CIIE mai taken "Sabon zamani, makoma mai kyau" a Shanghai wanda ake sa ran kammalawa a ranar 10 ga wata Nuwamba, kamfanoni kusan 3,900 daga kasashe da shiyyoyin duniya 155 ke halartar bikin baje kolin.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China