Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugaban Rwanda ya yi maraba da bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin
2019-11-09 15:49:09        cri
Shugaban Rwanda Paul Kagame, ya ce bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin, abu ne da suke farin ciki da shi, duba da cewa cinikayya na da muhimmanci ga tattalin arzikin kasashen 2 da ma duniya baki daya.

Paul Kagame ya bayyana a jiya, yayin wani taron manema labarai a birnin Kigali cewa, ga kasar Rwanda, dangantaka tsakanin kasa da kasa ko kuma tsakanin kasashe da dama kamar yankin cinikin mara shinge na Afrika, wanda ke hada kasashen Afrika su yi aiki tare da kungiyoyi ko kuma babbar kasa kamar Sin, abu ne mai matukar kyau kuma suke fatan ganin kasancewarsa.

Shugaban ya kara da cewa, yana sa ran ta hanyar baje kolin, Rwanda da kasashen Afrika su amfana daga harkokin cinikayya da kasar Sin. Yana mai cewa, ya kamata Sin da kasashen Afrika sun tabbatar cinikayya a tsakninsu ta amfane su, imma ta hanyar kasa da kasa ko kuma ta hanyar yankin cinikayya mara shinge na nahiyar Afrika. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China