Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ministocin lafiya na kasashen kudancin Afrika sun kulla kawance domin tunkarar cutar Ebola
2019-11-09 16:05:18        cri
Ministocin Kungiyar raya yankin kudancin Africa SADC, sun amince da kulla kawance domin yaki da cutar Ebola ta hanyar tunkara da shirya mata.

Ministar lafiya ta kasar Tanzania, Ummy Mwalimu, ta ce an yanke shawarar kulla kawancen ne a ranar Alhamis da dare, a karshen taron ministocin lafiya da yaki da cutar kanjamau na kasashe mambobin kungiyar SADC, a birnin Dar-es-salam, a cibiyar hada hadar kasuwanci ta Tanzania.

An yanke shawarar kulla kawancen ne yayin da Tanzania ke fuskantar barazana mai yawa na barkewar cutar Ebola, biyo bayan barkewar cutar a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo dake makwabtaka da ita, inda ya zuwa ranar 13 ga watan Oktoba, aka samu jimilar mutane 3,228 da suka kamu da cutar, inda daga cikinsu aka tabbatar da 3,114 sun kamu, yayin da kuma ta yi sanadin mutuwar mutane 2,123.

A watan da ya gabata ne hukumar lafiya ta duniya WHO, ta ce Tanzania ta gabatar da sabon rahoton shirinta na tunkarar cutar.

Rahoton ya nuna cewa daga watan Augustan 2018 kawo yanzu, an samu rahoton Ebola guda 29, inda aka gwada mutane 17, kuma sakamakon gwajin ya nuna babu cutar, ciki har da gwaje-gwaje 2 da aka yi a watan Satumban 2019. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China