Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
'Yan kasuwar Nijeriya sun yabawa bikin CIIE da Sin ta kira
2019-11-09 16:54:58        cri

Mataimakiyar jami'in dake kula da dangantaka tsakanin kasa da kasa ta cibiyar ciniki da raya masana'antu ta jihar Lagos na Nijeriya, Temitope Akintunde ta bayyana cewa, a halin yanzu, harkokin cinikayya tsakanin kamfanonin kasar Sin da mambobin cibiyar da suka halarci bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin, wato CIIE karo na biyu, na karuwa sosai. Ta ce lallai bikin CIIE ya samar musu damammakin ciniki da yawa, ya kuma bude musu kofar yin ciniki cikin kasuwannin kasa da kasa. Shi ya sa, a lokacin kamala bikin CIIE karo na farko, suka bayyana cewa, tabbas za su halarci bikin karo na biyu, sabo da sun karu sosai.

Madam Akintunde ta bayyana haka ne yayin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigo da su kasar Sin karo na biyu, wanda ke gudana a birnin Shanghai na kasar Sin. Inda a bana, ta sake jagorantar tawagar wakilai 'yan kasuwar Nijeriya don halartar bikin karo na biyu.

Ta kuma kara da cewa, jimilar mambobin cibiyar 13 ne suka halarci bikin baje kolin na bana, adadin da ya ninka kusan sau biyu idan aka kwatanta da na shekarar 2018.

Madam Akintunde ta kuma yaba matuka da bikin baje kolin da kasar Sin ta kira, tana mai cewa, kasar Sin ta kara shigo da kayayyakin kasashen waje, da kuma kara bude kofa ga waje, lamarin da ya nuna adawa mai karfi da kariyar ciniki da daukar ra'ayi na kashin kai. Har ila yau, ta ce aikin kara bude kofa ga waje da kasar Sin take yi a halin yanzu, zai taimakawa bunkasuwar tattalin arzikinta. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China