Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CIIE ya nuna kyawawan halayen kasuwannin Sin guda hudu
2019-11-09 17:00:28        cri

Cikin bikin baje kolin kayayyakin da ake shigowa da su kasar Sin da ke gudana a birnin Shanghai na kasar, kamfanonin kasa da kasa sun kawo sabbin kayayyakinsu mafi kyau zuwa bikin, domin shiga cikin kasuwannin kasar Sin, lamarin da ya nuna kyawawan halayen kasuwannin kasar Sin guda hudu. Wadanda suka hada da, karuwar bukatun al'ummomin kasar Sin da yawansu ya kai biliyan 1.4, da kayayyakin ababen more rayuwa da tsarin zirga-zirga masu inganci, da yanayin kasuwanci mai kyau da ake ci gaba da kyautatawa, da kuma bunkasar fasahohi bisa ci gaban da aka samu a fannin kimiyya da fasaha.

Haka kuma, an sami baki daga kasa da kasa cikin bikin baje kolin CIIE na 2, kuma ana fatan dukkansu za su cimma moriya, domin biyan bukatun al'ummomin kasa da kasa na jin dadin zaman rayuwa, wanda shi ne muhimmin burin kasar Sin na kara bude kofa ga waje. Bisa shirin da kasar Sin ta yi, cikin shekaru 15 masu zuwa, karfin kayayyakin da kasar Sin za ta shigo da su daga kasashen ketare zai wuce dalar Amurka biliyan dubu 30, a sa'i daya kuma, karfin harkokin hidima da kasar Sin za ta shigo da su zai wuce dalar Amurka biliyan dubu 10. Tabbas, kasuwannin kasar Sin masu bude kofa ga waje za su samar da karin damammakin ciniki da moriya ga kasa da kasa, da kuma ba da babbar gudummawa ga bunkasuwar tattalin arzikin duniya baki daya. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China