Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Iran ta zargi dakarun kawancen da Amurka ke jagoranta da laifin kawo rashin zaman lafiyar duniya
2019-11-10 15:30:46        cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Iran Abbas Mousavi, ya zargi dakarun tsaron da Amurka ke jagoranta da laifin gazawa har ma ta zarge su da haddasa rashin zaman lafiyar duniya, kamfanin dillancin labaran IRNA ya bada rahoton.

Mousavi ya yi Allah wadai da yunkuri na baya bayan nan da Amurkar ta yi na kafa wata rundunar tsaron teku ta hadin gwiwa a yankin Gulf, yana mai cewa Amurka tana amfanin da sauran kasashen duniya a matsayin karnukan farauta domin cimma burinta na kashin kai.

Jami'in na Iran ya bukaci kasashen dake shiyyar da su dauki kwararan matakan tabbatar da zaman lafiya da tsaron shiyyar ba tare da neman wani dauki daga kasashen ketare ba.

A ranar Alhamis ne, dakarun wadanda Amurka ke jagoranta suka kaddamar da shirinsu, bisa abin da suka kira da cewa, kare harkokin da suka shafi tekun yankin Gulf.

Washington ta ce an kafa hadakar ne don dakile dukkan barazar da zata iya kawo cikas wajen samar da albarkatun mai a duniya. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China