Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Shugabannin Turkiyya da Rasha sun tattauna batun Syria da kuma dangantakar dake tsakanin kasashensu
2019-11-10 15:47:25        cri
A jiya Asabar shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin, sun tattauna ta wayar tarho kan batun rikicin Syria da sauran batutuwa dake shafar dangantar dake Tsakanin kasashen biyu, ofishin shugaban kasar Turkiyya ya tabbatar da hakan.

Dukkanin shugabannin biyu sun jaddada aniyarsu game da batun yarjejeniyar Sochi wacce aka cimma matsaya kanta a ranar 22 ga watan Oktoba tsakanin Ankara da Moscow game da batun janyewar mayakan Kurdawar Syria daga yankunan dake kan iyakar Turkiyya a arewacin Syria.

Erdogan da Putin sun kuma tattauna kan matakan da za su dauka na sake karfafa dangantakar dake tsakanin kasashen biyu da kara yawan jarin cinikayyar dake tsakaninsu, a cewar fadar shugaban kasar. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China