Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Rahoto: Fannin fasaha ne ya samar da mafi yawan sabbin attajiran kasar Sin a 2018
2019-11-10 16:32:40        cri
Wani rahoto ya nuna cewa, fannin kamfanonin fasahar zamani a kasar Sin ya yi matukar bunkasa tattalin arzikin zamani a kasar, lamarin da samar da wasu sabbin hanshakan masu kudi a shekarar 2018.

A cewar rahoton wanda kamfanonin UBS da PwC suka fitar a ranar Juma'a, ya nuna cewa, daga cikin sabbin hamshakan masu kudi Sinawa na shekarar 2018, kashi 21 sun fito ne daga fannin fasahar zamani, yayin da kashi 7 ne kachal suka fito daga bangaren gina gidaje, fannin da a bisa al'ada shi ne ya saba samar da manya-manyan masu kudi a masana'antun kasar.

Rahoton ya bayyana biloniyoyi a matsayin mutanen da suka mallaki dukiyar da ta dara dalar Amurka biliyan guda.

Masu masana'antun kasar Sin sun shiga cikin jerin manyan attajiran duniya masu matsayi na biyu mafi girma ne cikin shekaru biyar da suka gabata.

"Manyan nasarorin da kasar Sin ta cimma wajen samar ta hanyoyin samun arziki babbar dama ce ga kamfanin UBS," a cewar Marina Lui, shugabar sashen gudanar da tattalin arzikin kamfanin UBS na kasar Sin, ta kara da cewa, kamfanin yana cigaba da lalibo wasu sabbin damammaki karkashin shirin bude kofa a harkokin kudade da gwamnatin Sin ke cigaba da aiwatarwa. (Ahmad)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China