Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Babban jamiin kasar Sin ya jaddada rawar da tsarin doka zai taka ga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya
2019-11-11 10:13:59        cri

Mamban hukumar kula da harkokin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS kuma shugaban kungiyar lauyoyi ta kasar Sin, Wang Chen, ya ce rawar da tsarin doka zai taka ga shawarar Ziri Daya da Hanya Daya muhimmin bangare ne na aikin ginin zirin tattalin arziki na hanyar siliki da hanyar siliki kan teku a karni na 21.

Wang Chen ya bayyana haka ne a jiya, yayin bikin bude dandalin tattaunawar hadin gwiwar kasa da kasa kan harkokin shari'a, a birnin Guangzhou na lardin Guangdong dake kudancin kasar Sin.

Kafin gabatar da jawabin, sai da jami'in ya karanta wasikar taya murnar bude taron da Shugaba Xi Jinping ya aike, inda ya ce wasikar ta nuna fatan kasar Sin na samar da yanayin shari'a mai kyau tare da hadin gwiwar kasa da kasa, da samar da kyakkyawar alkibla ga hadin gwiwar da kuma aiwatar da shawarar Ziri Daya da Hanya Daya.

Wang Chen ya ce a shirye kasar Sin take, ta aiwatar da musaya da hadin gwiwa a bangaren shari'a da kasashen dake kan zirin tattalin arziki na hanyar siliki da hanyar siliki kan teku a karni na 21 da cimma matsaya guda da tsara muradun da suke son cimmawa da samar da dandalin tattaunawa a fannin da kuma hada hannu wajen ganin hadin gwiwar ya samar da sakamoko. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China