2019-11-11 10:42:55 cri |
Shugaban kasar Ruwanda Paul Kagame ya bayyana cewa, a halin yanzu, ana fuskantar sauyin yanayi ta fuskar ciniki a duniya, kasar Ruwanda tana son hadin gwiwa da kawancen dake hada wasu kasashe, ko kuma yin hadin gwiwa da babbar kasa mai samun ci gaba a fannin tattalin arziki kamar kasar Sin. Kuma yana fatan kara moriyar da kasar Ruwanda da sauran kasashen Afirka za su samu, ta hanyar halartar bikin baje kolin CIIE da kasar Sin ta kira.
Haka kuma, masanin kasar Kenya Stephen Ndegwa ya gabatar da sharhi mai taken "A ganin kasar Kenya, kasuwanni a kasar Sin suna da kyau". Cikin sharhin, ya ce, kasar Sin ita ce babbar abokiyar ciniki ta kasar Kenya, kana, kasar Kenya ta sami gabilin jarin waje daga kamfanonin kasar Sin. Ko da yake, tana fuskantar rashin daidaito ta fuskar ciniki a tsakaninta da kasar Sin, amma, za ta warware wannan matsala ta hanyar kara fitar da hajoji zuwa kasar Sin, a maimakon, rage hajojin da za ta shigar kasar daga kasar Sin. Haka kuma, ya ce, bikin baje kolin CIIE ya samar wa kasar Kenya wata kyakkyawar dama wajen habaka kasuwannin kasar Sin masu kunshe da mutane biliyan 1.4. (Maryam)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China