Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD da Tanzania sun hada gwiwa don yaki da cin zarafin mata
2019-11-11 12:47:27        cri

Hukumar kula da al'amurran mata ta MDD mai fafutukar samar da daidaito a tsakanin jinsi da bunkasa sana'o'in dogaro da kai ga mata, ta yi hadin gwiwa da gwamnatin kasar Tanzania domin yaki da cin zarafin mata, wani babban jami'in hukumar ya tabbatar da hakan.

Faustine Ndugulile, mataimakin ministan lafiya da ci gaban al'umma, da kula da batun jinsi, da tsofaffi da kananan yara na kasar Tanzaniya ya ce, tun bayan da aka kaddamar da hadin gwiwar, adadin laifukan cin zarafin da ake yiwa mata ya yi matukar raguwa a kasar.

Jami'in ya ce, kimanin laifukan da suka shafi nuna wariya da cin zarafin mata 41,000 aka samu a fadin kasar cikin shekarar 2017, amma bayan yunkurin da aka yi karkashin hadin gwiwa tsakanin hukumar kula da al'amurran mata ta MDD da gwamnatin Tanzaniyan, matsalolin sun ragu matuka.

Hukumar kula da al'amurran mata ta MDD dake Tanzania ta shirya wani taron karawa juna sani a Dodoma, babban birnin kasar, domin zaburar da 'yan majalisu game da yadda za su ba da gudunmowarsu a yakin da ake da take hakkokin mata.

Ndugulile ya ce, a halin yanzu gwamnatin kasar tana shirin aiwatar da wani muhimmin shiri na shekaru biyar wato 2017/2018-2021/2022 da nufin lalibobi muhimman hanyoyin dakile laifukan cin zarafin mata.

Ndugulile ya bukaci 'yan majalisun dokokin kasar da su taimaka wajen kawo karshen munanan al'adu da suka shafi tsarin gargajiya a tsakanin al'umma wadanda ke kara rura wutar laifukan take hakkokin mata da nuna wariyar jinsi.(Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China