Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ma'aikatar harkokin wajen Sin: Wasu jami'an Amurka na da boyayyiyar manufarsu
2019-11-11 20:33:58        cri
Kwanan baya, a gun taron koli na yanar gizo na shekarar 2019 da aka shirya a kasar Portugal, wasu jami'an gwamnatin Amurka sun gargadi sauran kasashe da kada su yi amfani da na'urorin kamfanin Huawei na kasar Sin, sun kuma ce, gwamnatin kasar Sin ta yi amfani da na'urorin sadarwa na Huawei wajen satar muhimman bayanan kungiyar tarayyar kasashen Afirka wato AU a cikin shekaru biyar da suka gabata.

Game da haka, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang ya bayyana a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Litinin cewa, batun cewa wai "Sin tana sanya ido kan hedkwatar AU" labaran karya ne da kafofin watsa labarun yammacin duniya suka tsara, kuma jami'an gwamnatin Amurka suna da boyayyiyar manufa, yadda suka sake yayata cewa, wai "kasar Sin tana amfani da na'urorin Huawei don satar muhimman bayanan AU"

Geng ya sake nanata cewa, game da irin jita-jitar da Amurkan ke yayatawa, kasar Sin ta bayyana matukar adawa a kai, kuma abokanta na Afirka ma ba za su amince da su ba. Haka kuma bai kamata kasar Amurka ta nuna karfin ta na tayar da rade-rade fiye da kima ko kaskantar da karfin sauran kasashe ta yanke hukunci ba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China