2019-11-11 20:36:13 cri |
Da misalin sa'a daya da mintuna 26 da dakika 7 bayan tsakar daren, shagon na TMall ya sayar da kayayyakin da darajarsu ta kai Yuan biliyan 120.7, adadin da ya dara kayan da ya sayar a makamancin wannan rana a shekarar 2016.
Dukkan wannan alkaluma, sun kafa wani sabon tarihi a ranar gwagawaren, wanda shagon na TMall ya tsara a ranar 11 ga watan Nuwamban shekarar 2009.
A cewar kamfanin na Alibaba, sama da tanbarun kaya 22,000 na ketare daga kasashe da yankuna 200, sun shiga sayayyar wannan shekara a kasar Sin.
Wani mai bincike a cibiyar hadin gwiwar cinikayya da tattalin arzikin kasa da kasa dake karkashin ma'aikatar cinikiyya ta kasar Sin Zhou Mi, ya bayyana cewa, sabbin bayanan, sun nuna yadda tattalin arzikin kasar Sin ke kara karfi da fa'idar ci gaban fasahar zamani da cinikayyar kasa da kasa.(Ibrahim)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China