Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya yi shawarwari da shugabannin Girka
2019-11-12 10:05:11        cri

 

Jiya Litinin, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi shawarwari da shugaban kasar Girka Prokopis Pavlopoulos da firaministan kasar Kyriakos Mitsotakis a birnin Athens, fadar mulkin kasar Girka.

Cikin sanarwar karfafa dangantakar abota tsakanin kasashen biyu bisa manyan tsare-tsare da bangarorin biyu suka fidda a wannan rana, shugabannin biyu sun jaddada cewa, kasashen Sin da Girka za su ci gaba da inganta dangantakar abota tsakanin kasar Sin da kungiyar tarayyar kasashen Turai ta EU, domin kafa dangantaka irinta zaman lafiya, da karuwa, da karfafa kwaskwarima da kuma raya al'adu.

Cikin ganawar shugabannin biyu, Xi Jinping ya bayyana cewa, hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Girka bai kasance hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu kadai ba, domin har ya zama mu'amalar dake tsakanin manyan al'adu guda biyu. Ya ce ya kamata dukkanin bil Adama su kara kyautata halayensu, a maimakon nuna kashin kai da kuma neman moriyar da ba ta dace ba. Ya ce kasar Sin ta kan girmama kasa da kasa, kuma tana son neman ci gaba tare da kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa.

Bugu da kari, shugabannin biyu sun cimma ra'ayi daya kan gudanar shawarar "Ziri daya da hanya daya" cikin hadin gwiwa. Shugaba Xi Jinping ya ce, ya dace kasar Sin da kasar Girka su habaka ciniki da harkokin zuba jari dake tsakaninsu. Yana mai cewa, kasar Sin tana son shigar da karin amfanin gona daga kasar Girka, tana kuma sa kaimi ga kamfanonin kasar su zuba jari a kasar Girka. (Maryam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China