Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kamfanin Sin zai tallafawa aikin gina manyan hanyoyin da za su hade yankunan Sahara a Najeriya
2019-11-12 10:25:01        cri
Wani kamfanin gine-ginen kasar Sin ya sanar a jiya Litinin cewa zai ci gaba da taimakawa aikin gina manyan hanyoyin mota na shiyyar yankunan Sahara da aka tsara daga cikin Najeriya, da zarar an kammala ayyukan gina muhimman hanyoyin mota a cikin Najeriyar.

Aikin gina manyan titinan motar na yankunan Sahara muhimmin aiki ne da ya hade sassan nahiyar inda ya ratsa ta kasashen Afrika 6, da suka hada da Algeria, Chadi, Mali, Nijer, Najeriya, da Tunisiya. An tsara aikin ne da zummar bunkasa harkokin kasuwanci ta hanyar hanyoyin mota da kuma daga matsayin ci gaban shiyyoyin Afrika.

Da yake jawabi ga kamfanin dillancin labarai na Xinhua a gefen taron wuni biyu na kwamitin tsara gina manyan titinan mota na yankunan Sahara (TRLC), karo na 70, Zhang Wenfeng, manajan daraktan kamfanin CHEC dake Najeriya, ya bayyana aikin wanda aka tsara gudanarwa a matsayin daya daga cikin muhimman ayyukan da za su hade dukkan yankunan na shiyyoyin Afrika.

Ya ce aikin ba kawai zai inganta harkokin sufuri a Najeriya ba ne, har ma zai hada babbar hanyar mota ta kasa da kasa mafi girma a tsakanin shiyyoyin yammacin Afrika, tsakiyar Afrika, da arewacin Afrika, wanda hakan zai kara bunkasa yanayain hanyoyin mota a shiyyar. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China