Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwanciyar hankali a bangaren siyasa ya bada damar samun ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afrika
2019-11-12 10:31:08        cri
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Cyril Ramaphosa, ya ce kwanciyar hankalin da aka samu a bangaren siyasa a baya bayan nan a nahiyar Afrika, ya ba wasu kasashe damar samun ci gaban tattalin arziki da kuma zama wuraren dake jan hankalin masu zuba jari.

Da yake jawabi yayin taron zuba jari na Afrika karo na 2 a birnin Johannesburg, Cyril Ramaphosa ya ce dandalin taron, wanda ya samu halartar shugabannin Afrika 6, wuri ne da za a ingiza ci gaban nahiyar.

Ya ce taron ya hada gwamnatocin Afrika da asusan dake adana arikin kasashe da bankuna da bangarori masu zaman kansu da sauransu, domin su lalubo hanyoyin amfana daga damarmakin dake kunshe da tattalin arzikin nahiyar.

Ya kuma bada misali da gudanar zabuka lami lafiya a kasashen a Afrika ta kudu da Nijeriya da Malawi da Namibia da Botswana da Mozambique da sauran kasashen nahiyar, a matsayin alamar samun kwanciyar hankali.

Ya kara da cewa, kayayyakin more rayuwa muhimmai ne wajen ingiza ci gaban tattalin arziki, kuma suna bada muhimmanci kan neman zuba jari a bangaren, ta yadda za su cimma ajandar 2063 a fannin inganta zaman takewa da tattalin arziki da kuma muradun ci gaba masu dore na MDD. (Fa'iza Mustapha)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China