Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Fasahar Sin ta taimakawa ci gaban kasuwancin yanar gizo a Afirka
2019-11-12 10:50:46        cri

Yanzu haka Sinawa masu sayayya suna jin dadin sayayya a ranar gwagware wato ranar 11 ga watan Nuwamba, bikin sayayya na ranar gwagware na kasa da kasa a nan kasar Sin, a kasashen Afirka wadanda ke da nisan kilomita dubu goma kuwa, masu sayayya su ma suna jiran zuwa bikin.

A babban dakin adana kayayyaki na kamfanin kasuwanci ta yanar gizo na Kilimall dake karkarar Neirobi, fadar mulkin kasar Kenya, ma'aikata sama da dari daya suna gudanar da aiki tukuru, domin aike da kayayyakin dake cikin dakin zuwa ga wurare daban daban a fadin kasar, mai kula da aikin na kamfanin Peng Fu ya gaya mana cewa, wannan rana ta 11 ga watan Nuwamba a kowace shekara, sun fi shan aiki, adadin kayayyakin da suke aikawa a ranar ya kan karu har sau ninki biyar, idan aka kwatanta su da na yau da kullum.

An kafa kamfanin Kilimall ne a watan Yulin shekarar 2014, wanda ya kasance daya daga cikin manyan kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo a kasar ta Kenya, kawo yanzu kamfanonin samar da kayayyaki sama da dubu daya suna sayar da kayayyakinsu a dandalin, masu sayayyar da suke amfani da dandalin su ma sun kai fiye da miliyan 5, a don haka adadin wuraren da aka kebe domin adanawa da kuma aike kayayyaki a kasashen Kenya da Uganda da Najeriya su ma sun kai sama da dari daya. Yanzu a Kenya, matsakaicin adadin kayayyakin da ake sayarwa a dandalin Kilimall ya zarta dubu 5, adadin da ya kai kaso 30 bisa dari dake cikin kasuwar kasuwancin yanar gizo ta B2C wato Business-to-Consumer a Kenya.

Wani babban kamfanin kasuwanci ta yanar gizo na daban a nahiyar Afirka shine Jumia, wanda ya fara sayar da hannun jarinsa a cibiyar cinikin hada-hadar kudin New York na Amurka a watan Aflilun bana, an yi hasashen cewa, darajar kamfanin ya riga ya kai dalar Amurka biliyan 1, kana kamfanin Jumia kamfani ne na farko na nahiyar Afrika da aka kafa ta hanyar yin amfani da kimiyya da fasaha na zamani wanda yake sayar da hannun jari a Amurka, shi yasa ana kiransa da sunan "Amazon na Afirka", ko "Alibaba na Afirka".

Daya daga cikin masu kafa kamfanin Jumia Saha Boinonek ya gayawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, "A nahiyar Afirka, akwai wayoyin salula da masu amfanin yanar gizo da yawan gaske, kana abu mai faranta rai shine, adadinsu yana kara karuwa cikin sauri, a don haka mun ga babbar dama ta kasuwancinmu."

Babban sakataren kungiyar kasuwanci ta yanar gizo ta kasar Sin Peng Lihui wanda ya kai ziyara Kenya a watan Oktoban da ya gabata ya bayyana cewa, "Muna iya ganin babban ci gaban da kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo suka samu a kasashen Afirka daga salon sayayya kamar su hayar tasi ta wayar salula, da sayen abinci ta yanar gizo, da biyan kudi ta yanar gizo da sauransu."

Dalilin da yasa kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo na Afirka suka samu ci gaba cikin sauri shine domin kasar Sin ta samar da fasahohin da ta samu a bangaren gare su ta hanyar gudanar da hadin gwiwa dake tsakanin sassan biyu, saboda kasar Sin ta fi rinjaye a fannin kasuwanci ta yanar gizo.

Game da wannan, manajojin kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo na Afirka da dama sun jaddada cewa, da gaske ne sun more fasahohin kasuwanci ta yanar gizo na kasar Sin, kana suna sa ran cewa, kasar Sin zata horas da karin kwararrun masu tafiyar da harkokin kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo gare su ta hanyar hadin gwiwa dake tsakaninsu.

Daya daga cikin masu kafa kamfanin kasuwanci ta yanar gizo na HeHe na Ruwanda David Enshudi ya taba samun horaswa na kwas din "Abokai masu kafa kamfanonin kasuwanci ta yanar gizo" na tsawon makonni biyu da rukunin Alibaba na kasar Sin ya shirya a watan Mayun bana, ya gaya mana cewa, dandalin kasuwanci ta yanar gizo na Alibaba wato eWTP ya samar da dama ga kamfanonin Ruwanda domin su shiga babbar kasuwa a fadin duniya.

Jeremy Dutt, mataimakin shugaban zartaswa na kamfanin Jumia yace, yanayin yanar gizo mai inganci na kasar Sin ya burge shi matuka, yana sa ran kamfanonin kasar Sin zasu amfani babbar moriyar kasuwanci ta yanar gizo ta Afirka tare da Jumia.(Jamila)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China