2019-11-12 19:58:18 cri |
Shagon sayar da kayayyaki ta Intanet na rukunin kamfanin Alibaba wato TMall ya kara shigar da wasu sabbin tambarun kaya daga kasashen ketare, wadanda karuwar ta ninka sau uku bisa na makamancin lokacin bara, galibi daga Amurka, Burtaniya, Japan da kuma sauran kasashen yammacin duniya. Yadda suke kokarin neman shiga kasuwar kasar Sin, ya nuna cewa, maganar " raba gari ta fannin tattalin arziki" a tsakaninsu da kasar ta Sin, abu ne maras tushe, kuma ba zai faru ba.
Harkokin sayayya na taka muhimmiyar rawa ga ci gaban tattalin arziki. Don haka, babbar kasuwar cikin gida ita ce ginshikin tattalin arzikin kasar Sin wajen fuskantar kalubale daga ketare da ci gaba da yin kwaskwarima a gida da bude kofa ga ketare. (Ma'aikaciyar Sashen Hausa: Bilkisu Xin)
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China