Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Hadin kai a tsakanin Sin da Girka na kara inganta
2019-11-12 20:53:14        cri

 

An samu cikakkiyar nasara a ziyarar aikin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kai a kasar Girka a tsakanin ranakun 10 zuwa 12 ga wata. Wannan ya nuna cewa, yanzu dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni a tsakanin kasashen biyu bisa tushen mu'amalar wayin kai da hadin kan samun moriyar juna na karuwa, ko shakka babu, jama'ar kasashen biyu za su samu sabuwar damar ci gaba, tare kuma da ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Turai gaba.

 

 

Hadin kai a tsakanin Sin da Girka ba batu ne da ya shafi bangarorin biyu kawai ba, har ma zai yi muhimmin tasiri sosai ga dangantakar dake tsakanin Sin da Turai gaba daya. Bisa hadin kan kasashen biyu,kasar Sin za ta inganta hadin kai da kasashen dake gabashi da ma tsakiyar Turai bisa shawarar "Ziri daya da hanya daya", hakan zai taimaka wajen gaggauta hadewar da juna a tsakanin kasashen yankin Turai da na Asiya. Nasarar da kasar Sin ta cimma kan wasu ayyukan da ta gudanar a Girka, za ta taimaka wajen kawar da damuwar da wasu kasashen Turai ke nunawa kan zuba jari a kasar Sin, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakanin Sin da Turai gaba. (Ma'aikaciyar Sashen Hausa: Bilkisu Xin)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China