Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sharhi:Kada a gurgunta fahimtar sakon da aka samar kan batun Hong Kong
2019-11-16 17:05:37        cri

A yayin da ya halarci taron shugabannin kasashen BRICS karo na 11 a birnin Brasilia a kwanakin baya, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya yi nuni da cewa, laifukan da ake ta aikatawa a Hong Kong na nuna karfin tuwo da tsattsauran ra'ayi sun lalata tsarin doka da oda, da ma kwanciyar hankali da ci gaban yankin, wanda kuma ya kalubalanci ka'idar kasa daya mai tsarin mulki biyu. Kawo karshen tarzoma tare da maido da oda, aiki ne na gaggawa kuma na farko da ke gaban Hong Kong, za mu ci gaba da goyon bayan hukumar yankin musamman na Hong Kong ta gudanar da mulkinta bisa doka, kuma 'yan sanda su tafiyar da ayyukansu yadda ya kamata, sa'an nan hukumomin shari'a na Hong Kong ma su hukunta masu laifuka yadda ya kamata. Ko kadan gwamnatin kasar Sin ba za ta sauya niyyarta ta kiyaye ikon kasa da tsaro da ci gabanta, da niyyarta ta aiwatar da manufar kasa daya mai tsarin mulki biyu, da kuma niyyarta ta kin yarda da katsalandan daga kasashen wajen cikin harkokin Hong Kong ba.

Jawabin Shugaba Xi Jinping ya bayyana ainihin gaskiyar lamuran da ke faruwa a Hong Kong da ma illolin da suka haifar, ya kuma bayyana matsayin gwamnatin kasar Sin na goyon bayan hukumar yankin musamman na Hong Kong wajen daidaita batun yankin bisa doka, baya ga haka, ya kuma bayyana niyyar gwamnatin kasar Sin ta kiyaye ikon kasar. Wannan shi ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya yi jawabi a fili dangane da rikicin Hong Kong da illolinsa da ma matsayin gwamnatinsa da niyyarta, ya kuma isar da sako ga kasa da kasa a kan batun.

Batun Hong Kong harka ce ta cikin gidan kasar Sin, kada kuma a raina wa niyyar kasar Sin ta kiyaye ikonta da ma tsaronta da ci gabanta, kada kuma a gurgunta fahimtar sakwannin da gwamnatin kasar Sin ta samar kan batun Hong Kong. (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China