Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ayyukan masu tsattsauran ra'ayi a yankin Hong Kong sun kawo illa ga manyan fannoni uku
2019-11-17 20:23:51        cri
A yayin ganawa ta 11 a tsakanin shugabannin kasashen kungiyar BRICS da aka yi a Brasilia, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada cewa, ayyukan masu tsattsauran ra'ayi da suka tsananta a yankin Hong Kong sun kawo illa ga tsarin dokoki da odar zamantakewar al'umma, da zaman lafiya da na karko a yankin, da kuma keta ka'idojin tsarin kasa daya amma da tsarin mulki biyu. Wadannan fannoni uku sun nuna babbar illa da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi suka kawo, da kuma shaida wa kasa da kasa hakikanin yanayin da ake ciki a yankin Hong Kong.

An yi nuni da cewa, masu tsattsauran ra'ayi sun keta tsarin dokoki da odar zamantakewar al'umma, tilas ne a yanke hukunci gare su. Sun tuntubi kungiyoyin kasashen waje masu kin amincewa da Sin da keta mutuncin kasar da ka'idojin tsarin kasa daya amma da tsarin mulki biyu, wanda kowace kasa ba za ta amince da shi ba.

An kara da cewa, wannan ne karo na farko da shugaban kasar Sin ya yi bayani game da babbar illa da ayyukan masu tsattsauran ra'ayi suka kawo wa yankin Hong Kong, da gabatar da aikin dakatar da ayyukan da mayar da doka da odar yankin, wanda ya shaida hanyar da za a bi don tabbatar da tsaron yankin Hong Kong. (Zainab)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China