Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasar Sin na kara karfin tinkarar matsalar ganin nesa da yaran kasar ke fuskanta
2019-12-03 15:08:34        cri

Matasa da yara masu yawa na fuskantar matsalar ganin abubuwa masu nisa, wannan ya kasance batun dake jawo hankulan bangarori daban daban a nan kasar Sin. Game da haka, wani jami'in ma'aikatar ba da ilmi ta kasar ya bayyana cewa, za a kara lokacin darussan wasannin motsa jiki da na motsa jiki bayan tashi daga karatu, don rage matsin da daliban makarantun firamare ke fuskanta a harkokinsu na karatu, kana da gudanar da ayyukan inganta lafiyar daliban dake makarantun firamare da na sakandare a fannonin kara ingancin malamai, kara wuraren motsa jiki, samar da na'urori da kuma kaddamar da tsare-tsare da dai sauransu. 

Alkaluma sun nuna cewa, a shekarar 2018, yawan matasa da yara dake fama da matsalar ganin abubuwa masu nisa ya kai kashi 53.6 cikin dari. A ranar 30 ga watan Agustan shekarar nan kuma, hukumomi guda takwas, ciki har da ma'akatar ba da ilmi sun hada kai don kaddamar da shirin gudanar da ayyukan yin rigakafin matsalar ganin abubuwa masu nisa da yara da matasa ke fama da ita. Shugaban sashen kula da harkokin motsa jiki da kiwon lafiya da ba da ilmi da fasaha na ma'aikatar mista Wang Dengfeng ya bayyana cewa, dalilan dake haddasa wannan matsalar suna da yawa, wanda ya fi tsanani shi ne, yadda ake amfani da idanu na dogon lokaci. Wang ya ce,

"Muhimmin dalili shi ne, harkokin karatu masu yawa da dalibai ke yi, dalibai su kan shafe lokuta da yawa suna karatu a ko wace rana, ban da wannan kuma, su kan yi amfani da kayayyakin masu amfani da lantarki na dogon lokaci, kamar wayar salula da kamputa da dai sauransu. "

Mista Wang ya kara bayyana cewa, ba a samu isasshen lokaci na motsa jiki bayan an tashi daga aji, musamman ma motsa jiki a waje, wanda kuma wani muhimmin dalili ne da ke haddasa matsalar ganin abubuwa masu nisa ga matasa da yara. A shekarar nan da muke ciki, kasar Sin ta kaddamar da shirin kula da lafiya daga shekarar 2019 zuwa 2030, inda aka ba da tabbacin gudanar da ayyukan, tare kuma da yin tsare-tsare kan burin da ake fatan cimmawa da hakikanan matakan da za a dauka. Baya ga haka, mista Wang ya bayyana cewa, a yanzu haka ma'aikatar ba da ilmin ta kasar Sin na jagorantar wani shiri da nufin inganta lafiyar daliban makarantun firamare da sakandare, wato a kara lokacin kwasa-kwasan motsa jiki da na motsa jiki bayan an tashi daga aji, da rage lokutan karatun dalibai, da kuma bullo da tsare-tsare iri daban daban don tabbatar da wadannan matakan biyu. A cewar mista Wang,

"A fannin kwasa-kwasan motsa jiki, takarda mai lamba 7 da kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta fitar ta tabbatar da cewa, daga aji na 1 zuwa aji na 3 na makarantun firamare, za a bullo da kwasa-kwasan motsa jiki na tsawon mintoci 160 a ko wane mako, sannan daga aji na 4 zuwa na 6 da dukkan azuzuwan makarantun midil kuma, kwasa-kwasai za su kai mintoci 150 a ko wane mako, a manyan makarantun sakandare da jami'o'i kuma, zai kai mintoci 120 a ko wane mako. Ban da wannan kuma, mun bukaci dukkan dalibai su rika motsa jiki na tsawon sa'a 1 a makarantunsu a ko wace rana. A cikin takardar game da yin rigakafi kan matsalar ganin abubuwa masu nisa da aka kaddamar a baya bayan nan, an kara wani sabon abu a cikin, wato akwai bukatar a kara sa'o'i 1 zuwa 2 ana motsa jiki bayan tashi daga makaranta, wato ke nan an gabatar da wata sabuwar bukata ga iyalai."

Domin tabbatar da hakan, makarantun kasar Sin suna bincike don neman hanyar da ta dace a wannan fannin. Shugaban makarantar sakandare na Xishan na lardin Jiangsu na kasar Sin, mista Tang Jiangpeng ya bayyana cewa, tun daga shekarar 2015, makarantarsa ta soma bullo da tsarin kwasa-kwasan motsa jiki, sannan dalibai 1500, za su iya amfani da na'urorin da aka samar a dakin motsa jiki na makarantar. Mista Tang ya ce,

"Sakamakon ruwan sama da ake yi a yankin kudancin kasar Sin, hakan ya sa, dalibai ba sa samun lokuta masu yawa don su rika motsa jikinsu a waje. Bisa wannan yanayin da ake ciki, na yi ta kokarin neman samun jari daga wajen gwamnatin wurin ta yadda za a gina ingantattun dakunan wasannin motsa jiki, ta yadda dalibai za su samu isassun dakunan motsa jiki na zamani. Bayan kokarin da muka yi, yanzu dakin wasannin motsa jiki na makarantarmu babu kamar sa a duniya, muna da dakin wasannin motsa jiki, dakin iyo, dakin wasan takwabi, dakin kokawar zamani ta taekwondo, dakin wasan yoga da dai sauransu."

Baya ga wadannan matakan da aka dauka kuma, an bukaci shigar da halin kiwon lafiyar dalibai cikin jarrabawar da aka yi wa makarantu a fannin kimanta ayyukansu.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China