Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Yawan wadanda suka rasu sakamakon rushewar gini a Kenya ya kai mutum 10
2019-12-09 09:45:44        cri

Rahotanni daga birnin Nairobin kasar Kenya na cewa, yawan wadanda suka rasu sakamakon rushewar wani gini a birnin ya kai mutum 10, bayan da a jiya Lahadi, aka gano karin gawawwakin mutum 4 da hadarin ya rutsa da su. Ginin dai ya rushe ne a ranar Juma'a inda nan take ya hallaka mutane 6.

Kwarrau na cewa ana samun ci gaba cikin sauri a fannin gine-ginen gidaje a Kenya, inda a ko da yaushe ake bude sabbin ayyukan gine-gine daban daban a kasar. To sai dai kuma duk da wannan ci gaba, a hannu guda, karuwar gidajen dake rushewa musamman a lokutan damuna, na nuni ga irin raunin kwarewa da sashen ke fuskanta. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China