Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kafofin yada labarai na kasashen Yamma na nuna halin ko in kula kan wasu ayyukan yaki da ta'addanci a Xinjiang
2019-12-09 15:57:16        cri

Kwanan baya, kamfanin telibijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN, karkashin jagorancin babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG, ya gabatar da wani fim dake bayyana labarai na Turanci, mai sunan "Xinjiang, fagen daga na yaki da ta'addanci a kasar Sin" da "Bakin hannu: Alakar kungiyar Islamic Ta Turkestan Ta Gabas da ta'addanci a Xinjiang", don bayyana ayyukan ta'addanci na rashin imani da 'yan ta'adda, da masu tsattsauran ra'ayi suka aikata a Xinjiang, da kuma kokarin da Sin take gudanarwa wajen yaki da su. Amma, wasu kafofin watsa labarai na kasashen yamma na yin fuska biyu kan wannan al'amari, inda suka yi biris da wadannan fina-finai, kamar dai ba su ji ba su gani ba.

Tabbatar da zaman lafiya da karko a Xinjiang aiki ne mai matukar wuya, kuma muhimmin aiki ne daga cikin ayyukan yaki da ta'addanci na duniya. Wadanda suke mai da hankali sosai kan bunkasuwar Xinjiang, da kare hakkin kananan kabilu a wurin, na iya fahimtar hakikanin halin da ake ciki a Xinjiang bisa wadannan fina-finai.

Jihar Xinjiang ta kasar Sin ta ba da gudunmawarta matuka ga ayyukan yaki da ta'addanci a duniya, kuma ba wanda zai iya mantawa da ita a wannan fanni. Kasar Sin na fatan 'yan siyasa na kasashen yamma, wadanda suke nuna tamkar sun makance kan wannan batu za su daina yin kurkure da suke aikatawa. Kuma idan sun ci gaba da karawa 'yan ta'adda da masu tsattsauran ra'ayi kwarin gwiwa, to kuwa za su yi girbin abubuwan da suka shuka. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China