Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Sin: Amurka na kokarin kawo cikas ga matakin daidaita takaddama
2019-12-09 20:06:56        cri

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Hua Chunying ta bayyana cewa, yayin da Amurka ke ci gaba da hana zabar wani reshe na kungiyar cinikayya ta duniya, alkali daya ne kawai zai kasance a reshen wannan kungiya a ranar 10 ga watan Oktoba, hakan ka iya zama mai wahalar gaske ga sashin dake daidaita takaddama ya gudanar da aikinsa yadda ya kamata, matakin da ka iya yin mummunar illa da hukumar da ma tsarin kasancewar bangarori daban-daban.

Galibin mambobin WTO dai, sun yi Allah wadai da yadda ake take tsarin kasancewar bangarori daban-daban.

Uwar gida Hua Chunying, ta bayyana cewa, taron ministocin harkokin wajen kungiyar G20 da na masu ruwa da tsaki na baya-bayan nan, duk sun bayyana damuwa matuka kan wannan batu, inda suka yi kira da a dauki mataki ba tare da bata lokaci ba, don ceto wannan tsari daga shiga mawuyacin hali.(Ibrahim)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China