Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
CGTN: Ko 'yan majalissar dokokin Amurka na fatan zama kakakin 'yan ta'adda ?
2019-12-10 10:05:53        cri

Kwanan baya, kamfanin telibijin na kasa da kasa na kasar Sin CGTN, karkashin jagorancin babban gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG, ya gabatar da wasu fina finai biyu dake bayyana labarai na Turanci, wadanda aka yiwa lakabi da " Ko 'yan majalissar dokokin Amurka na fatan zama kakakin 'yan ta'adda?"

Babban kamfanin gidan rediyo da telibijin na kasar Sin CMG, wanda ya rawaito hakan ya ce, fina finan sun nuna irin mummunan tasiri da ayyukan 'yan ta'dda da masu tsattsauran ra'ayin addini ya haifar a jihar Xinjiang ta kasar Sin, lamarin da ya daga hankalin kowa a cikin kasar Sin da ma kasashen waje.

To sai dai kuma a hakikanin gaskiya, wasu 'yan majalissar dokokin Amurka sun rika sukar tsarin yaki da ayyukan ta'addanci da kawar da tsattsauran ra'ayi da ke gudana a Xinjiang, suna yin fuska biyu wajen ba da kariya ga wadannan munanan akidu, matakin dake tabbatar da cewa, da gangan ko bisa kuskure, suna kokarin zama kakaki ga 'yan ta'adda.

Sharhin na CMG ya gabatar da tambayoyi don gane da wannan lamari, ciki hadda ko shin za a iya kidaya harin 11 ga watan Satumba da ya auku a Amurka a matsayin aikin ta'addanci? Shin ayyukan yaki da ta'addanci da Sin ke aiwatarwa ba domin kare hakkokin al'umma ba ne?

Daga karshe, sharhin ya ce idan har irin wadannan 'yan siyasa na Amurka suka dage su goyi bayan aikata laifuka, to kuwa ko shakka babu tarihi zai yi ramuwar gayya a kan su. (Saminu Alhassan)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China