Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kasashe mambobin ACP sun fara taro a Kenya
2019-12-10 10:34:53        cri
Kasashe mambobin kungiyar shugabannin Afirka da Caribbean da Fasifik ko ACP a takaice, sun fara gudanar da taron su na 9 a birnin Nairobin kasar Kenya, inda suka yi kira da a dauki matakan bunkasa tsarin cudanyar cinikayya bisa daidaito, don samar da ci gaba na bai daya, da zaman lafiya tsakanin kasashe masu tasowa.

Da yake jawabi yayin bikin bude taron na jiya Litinin, shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, wanda kuma a wannan karo ya karbi ragamar jagorancin kungiyar ta ACP na tsawon shekaru 3, ya ce ya kamata a karfafa dokokin cudanyar sassan duniya, ta yadda hakan zai magance kalubale da dama da ake fuskanta, ciki hadda talauci, da tashe tashen hankula, da tsattsauran ra'ayi, da batun sauyin yanayi.

A nasa jawabi kuwa, babban sakataren kungiyar Patrick Gomes, cewa ya yi taron na birnin Nairobi, ya samar da wani zarafi na jaddada burin kasashe masu tasowa, game da amfana daga damammakin dake akwai na ciyar da kan su gaba, da martaba doka da oda, da inganta tsarin cudanyar kasa da kasa, da samar da kyakkyawan jagoranci, da zaman lafiya da lumana.

Mahalarta taron na wannan karo wanda aka yiwa lakabi da "Sabuwar manufar ACP ta inganta cudanyar sassa daban daban", sun hada da shugabannin kasashe 17, da wakilai 70 daga kasashe mambobin kungiyar 79. Kaza lika wasu ministoci da wakilan hukumomin MDD, da jagororin kamfanoni, da masana da dama sun halarci wannan taro. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China