Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kwararrun kasashen waje sun ziyarci Hangzhou don samun kwarin gwiwa game da kare hakkin dan adam
2019-12-10 10:44:00        cri
Ziyarar yankin gabashin kasar Sin ta samar da sabon tunani game da batun kare hakkin bil adama ga wasu jami'ai da kwararru daga kasashe masu tasowa sama da 70 da wakilan MDD.

A ranakun Lahadi da Litinin, wakilai daga kasashen Asiya, Afrika da Latin Amurka, da jami'an MDD sun ziyarci Hangzhou, babban birnin lardin Zhejiang dake gabashin kasar Sin, kafin halartar taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashe masu tasowa kan batun kare hakkin dan adam na shekarar 2019 dake tafe.

A kasar Sin, amfani da fasahohin zamani wajen hada-hadar kasuwanci ta hanyar intanet da biyan kudi ta hanyar wayoyin hannu sun taimaka wajen inganta rayuwar al'umma da kyautata shirin kare hakkin dan adam, Jean Claude Mokeni, tsohon shugaban kwamitin kula da harkokin waje na majalisar dattijan jamhuriyar demokaradiyyar Kongo (DRC) ya bayyana hakan.

Shi ma a nasa tsokacin, Cesar Rodrigo Landa Arroyo, tsohon shugaban kotun shirya dokokin tsarin mulkin Peru ya ce, ya gamsu matuka bisa yadda kasar Sin ke aiwatar da muhimman ayyukan dake kyautata rayuwar al'ummun dake tsoffin yankunan dake makwabtaka da kasar. Wannan wata alama ce dake kara bayyana irin ci gaban da kasar Sin ta samu wajen kare hakkin dan adam.

A bisa yarjejeniyar Beijing wacce aka amince da ita a taron dandalin hadin gwiwar Sin da kasashe maso tasowa game da kare hakkin dan adama karo na farko da aka gudanar a Beijing a 2017, mahalarta taron sun yi amanna cewa samar da hakkin rayuwa da bunkasa ci gaba su ne muhimman tushen tabbatar da kare hakkin dan adam.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China