2019-12-10 10:56:20 cri |
Leo Atakpu, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron karawa juna sani na shiyya da ya gudana a birnin Nairobin kasar Kenya, ya ce yawa-yawan al'ummar nahiyar ba su ma fahimci mene ne ma'anar cin hanci ba, duba da yadda masu aikata shi ke zuba jari a sassa daban daban, suna samar musu da guraben ayyukan yi. Don haka a cewar sa, akwai bukatar fadakar da al'ummar nahiyar hanyoyin kandagarkin ayyukan cin hanci, da mummunan tasirin da yake yi ga tattalin arziki da ma rayukan su.
Atakpu ya kara da cewa, furta manufar yaki da cin hanci kadai ba zai wadatar ba, har sai an hada da aiki tukuru, ganin yadda da yawa daga al'ummar nahiyar ke da karancin fahimta a kan hakan.
Taron wanda aka bude a jiya Litinin, ya samu halartar kungiyoyi masu zaman kan su, wadanda suka zo daga sassan nahiyar da dama. (Saminu Alhassan)
| ||||
® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China