Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Furucin Shugaba Xi Jinping kan yadda aka samu nasara a Macao bisa manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu"
2019-12-17 14:45:54        cri

Daga ranar 18 zuwa ranar 20 ga wata, Xi Jinping, babban daraktan kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin, shugaban kasar, kana shugaban kwamitin aikin soja na kasar zai ziyarci yankin Macao don halartar bikin murnar cika shekaru 20 da dawowar yankin karkashin ikon kasar Sin, da bikin rantsar da gwamnatin yankin karo na biyar da za ta yi, gami da rangadin aiki a yankin. Shugaba Xi ya ziyarci Macao shekaru biyar da suka gabata, inda shi da mazauna yankin suka yi murnar cika shekaru 15 da dawowar yankin karkashin ikon kasar Sin, da waiwayar yadda aka raya yankin tun bayan dawowarsa, tare da tsara shirin samun dauwamammen ci gaba a nan gaba a karkashin manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu".

"ci gaba da raya manufar 'kasa daya amma tsarin mulki biyu', nauyi ne da ya rataya a wuyan gwamnatin tsakiya ta Sin, da gwamnatin yankin musamman na Macao, da al'ummomin kalibu daban daban na kasar ciki har da mazauna yankunan HongKong da Macao. Duk wata wahala da kalubalen da za mu fuskanta, babu wanda zai canza kudurinmu na bin wannan manufa, za mu ci gaba da himmatuwa wajen raya ayyuka bisa wannan manufar ba tare da kasala ba."

Shugaba Xi Jinping ya yi wannan furuci ne a ranar 20 ga watan Disamban shekarar 2014, yayin bikin murnar cika shekaru 15 da dawowar yankin karkashin ikon kasar Sin, da bikin rantsuwar kama aiki na gwamnatin yankin karo na hudu, wanda ya samu karbuwa sosai daga wajen mahalarta bikin.

Tun bayan dawowar yankin karkashin ikon kasar Sin, ana aiwatar da manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" da kuma babbar dokar yankin Macao yadda ya kamata, lamarin da ya aza harsashi mai inganci ga ci gabansa. Amma yadda za a yi amfani da damar bunkasar Sin a wannan sabon zamanin da ake ciki wajen kara karfin ci gaban Macao, shi ne muhimmin batu da ke gaban yankin.

A gun bikin murnar cika shekaru 15 da dawowar Macao karkashin ikon kasar Sin, shugaba Xi ya bayyana fata guda hudu domin karawa mazauna yankin kwarin gwiwar yada fifikon manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" wajen samun saurin ci gaba tare da babban yankin kasar. Yana mai cewa,

"A nan, ina so in bayyana fata guda hudu, wato na farko, a kara nuna himma da kwazo wajen kyautata kwarewar tafiyar da harkokin Macao. Na biyu, a tsara shiri wajen sa kaimi ga tattalin arzikin yankin, ta yadda zai samu dauwamammen bunkasuwarsa a fannoni daban daban yadda ya kamata. Na uku, a yi kokarin samun jituwa da kwanciyar hankali a zamantakewar al'ummar yankin. Na karshe kuma shi ne, a dora muhimmanci kan ilimantar da matasa don kago makoma mai kyau."

A cikin sa'o'i 28 da shugaba Xi ya kai ziyara a yankin Macao, ya halarci muhimman harkoki 15. Yayin da yake tattaunawa da sassa daban daban na yankin, ya sha nuna cewa, tsayawa tsayin daka kan manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu" abu ne da ya wajaba wajen samun wadata da zaman karko a HongKong da Macao cikin dogon lokaci, haka kuma wani muhimmin bangare ne wajen cimma babban burin farfado da al'ummar Sin, lamarin da ya dace da babbar moriyar kasa da al'umma, da ma muradu masu dorewa na HongKong da Macao daga dukkan fannoni. Xi ya kara da cewa,

"Yadda aka raya yankin Macao tun bayan dawowarsa karkashin ikon kasar Sin ya shaida cewa, muddin aka bi hanyar dai-dai, da aiwatar da manufar da ta dace, da daukar matakai yadda ya kamata, da ma hadin kan al'umma, to za a iya samun babbar nasara, kamar yadda Sinawa kan ce, za a iya nuna wasan kwaikwayo mai kyatarwa a kan babur ba sai a dandali ba. Baya ga kwarin gwiwa da karfi daga nasarorin da Macao ya samu, ya kamata mu gano sabon abubuwa da yanayin yanki ke ciki, domin tsara matakan kara samun ci gaba a nan gaba."

Game da yadda za a sa kaimi ga sha'anin da ya shafi manufar "kasa daya amma tsarin mulki biyu", Xi ya bayyana cewa,

"Dole ne a martaba wannan babbar manufa, da ma kiyaye 'yanci da tsaro da muradun bunkasar kasa, domin tabbatar da samun wadata da zaman lafiya a HongKong da Macao cikin dogon lokaci. Ban da wannan kuma dole ne a martaba ka'idar tafiyar da harkokin yankin HongKong da na Macao bisa doka, ta yadda za a martaba manufar 'kasa daya amma tsarin mulki biyu' yadda ya kamata. Haka zakila ya kamata a hada manufar kasar Sin daya tak a duniya da girmama bambancin tsarin mulki biyu, da kiyaye 'yancin gwamnatin tsakiya da hakkin tafiyar da harkokin yankunan biyu cikin 'yanci, da ma yada amfanin babban yankin kasar Sin na goyon baya da kyautata karfin takarar HongKong da Macao gaba daya, bisa la'akari da bambancin dake tsakaninsu."(Kande Gao)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China