Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Jakadan Sin dake Najeriya ya gana da ministan harkokin wajen kasar
2019-12-18 16:45:51        cri
Jiya Talata, jakadan kasar Sin dake Najeriya Zhou Pingjian ya gana da ministan harkokin wajen kasar Geoffrey Onyeama.

A yayin ganawar, Zhou ya ce, a sakamakon kokarin da bangarorin biyu suka yi, kasashen biyu sun kara amincewa da juna a fannin siyasa da samun gagaruman nasarori a hakikanin hadin kai, da nuna goyon baya ga juna. Zhou ya kara da cewa, kasarsa na son kara hada kai da bangaren Najeriya, da tabbatar da nasaroin da aka cimma a taron koli na Beijing na dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana da raya shawarar "Ziri daya da hanya daya" yadda ya kamata, da nufin cimma nasara da samun ci gaba tare.

A nasa bangaren, Geoffrey Onyeama ya bayyana cewa, kasar Sin muhimmiyar abokiyar hadin kan kasar Najeriya ce, shugaba Buhari da gwamnatinsa suna dora muhimmanci sosai kan bunkasa dangantaka da Sin. Ya ce bangaren Najeriya yana godiya sosai ga goyon bayan da Sin ta samar mata a fannin gina kayayyakin more rayuwa da ci gaba a fannoni daban daban, yana kuma fatan kara yin cudanya da Sin don zurfafa hadin kai a dukkan fannoni, ta yadda za a ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba. (Bilkisu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China