Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci bikin murnar cika shekaru 20 da maido da yankin Macao karkashin mulkin kasar Sin
2019-12-20 15:37:48        cri





A yau Jumma'a 20 ga wata, yankin musamman na Macao ya cika shekaru 20 da komawa karkashin ikon kasar Sin. Da safiyar wannan rana, an gudanar da bikin murnar ranar, da ma bikin rantsar da sabuwar gwamnatin yankin, inda babban sakataren kwamitin kolin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kana shugaban kasar, Mr. Xi Jinping ya hallara tare da gabatar da muhimmin jawabi.

A jawabin da ya gabatar, ya jaddada cewa, nasarorin da aka cimma a yankin Macao sun shaida cewa, muddin an aiwatar da manufar "kasa daya da tsarin mulki biyu" yadda ya kamata, manufar za ta kai ga taka rawar gani. Bayan da kasar Sin ta maido da ikonta a yankunan Hong Kong da Macao, harkokin yankunan harkokin cikin gida ne na kasar ta Sin, ba bukatar tsoma baki a cikin su. Da misalin karfe 10 na safiyar yau Jumma'a, aka kaddamar da bikin, inda aka rantsar da Ho Iat Seng, a matsayin sabon kantoman yankin musamman na Macao a gaban shugaba Xi Jinping.

Mr.Ho Iat Seng ya fuskanci tutar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, da ta yankin musamman na Macao, kuma ya daga hannunsa na dama, ya yi rantsuwar kama aiki, kamar yadda dokar yankin musamman na Macao ta tanada. Bayan kammala rantsuwar, Xi Jinping da Ho Iat Seng sun yi musafaha da juna. Daga nan kuma, a gaban shugaba Xi Jinping, manyan jami'an gwamnatin yankin musamman na Macao suka yi rantsuwar kama aiki karkashin jagorancin Ho Iat Seng.

Shugaba Xi Jinping ya kuma gabatar da muhimmin jawabi a wajen bikin, inda ya ce, a cikin shekaru 20 da kasar Sin ta maido da ikonta a yankin Macao, an bude wani sabon babi na tarihin yankin. Ya ce, an kiyaye tsari da oda a yankin Macao, bisa tushen tsarin mulkin kasar Sin, da ma dokar yankin Macao, kuma tsarin gudanar da harkokin yankin na dada inganta. Ya kara da cewa, a cikin shekarun 20 da suka wuce, an samu gagarumin ci gaba ta fannin raya tattalin arzikin yankin, kuma zaman rayuwar mazauna yankin ma ya kara kyautatuwa, har ma yankin ya zama na biyu a duniya ta fannin alkaluman GDP kan kowane mutum. Har ila yau, an kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin yankin, abin da ya sa Macao ya kasance daya daga cikin birane mafi tsaro a duniya.

Shugaba Xi Jinping ya jaddada cewa, ci gaba da nasarorin da yankin Macao ya samu sun shaida cewa, muddin aka nuna imani ga manufar "kasa daya da tsarin mulkin biyu", hakika za ta kara taka rawar a-zo-a-gani.

"A yayin da ake aiwatar da manufar 'kasa daya da tsarin mulki biyu', gwamnati gami da bangarori daban-daban na yankin Macao, suna tsayawa tsayin daka wajen kare 'yancin kasar Sin, da tabbatar da tsaro da ci gaba da kuma muradunta, a yayin da suke kuma kokarin kiyaye bunkasuwa da kwanciyar hankali a yankin Macao, kuma sun kare aniyarsu ba tare da kasala ba. Haka kuma suna more irin damammaki, da manyan tsare-tsare, gami da manufofin ci gaba da kasarsu ta Sin ta samar, inda suke neman ci gaban kansu da na kasa baki daya."

A jawabinsa, shugaba Xi Jinping ya kuma bayyana fatansa na ganin ci gaban Macao ta wasu fannoni hudu, ya ce yana fatan ganin sabuwar gwamnatin yankin musamman na Macao, da bangarori daban daban na al'ummar yankin, za su kara inganta gudanar da harkokin yankin, da ciyar da tattalin arziki gaba yadda ya kamata, da kara bada tabbaci, da kyautata zaman rayuwar jama'a, da kara inganta zaman lafiya da kwanciyar hankali tsakanin a'umma, don inganta ci gaban yankin zuwa wani sabon matsayi.

Shugaban ya ce, ya kamata gwamnatin yankin musamman na Macao, ta maida hankalinta kan abubuwan da ke damun mazauna yankin, ta yi kokarin daidaita batutuwan da suka shafi gidajen kwana, da kiwon lafiya da ciyar da tsoffi, kuma ta kara ba da taimako ga masu karamin karfi. Har wa yau, ya kamata ta dinga kyautata harkokin ba da ilmi, kuma ta samar da muhalli mai kyau ga matasa da ke tasowa. Ya ce, ya kamata a kiyaye al'adar hadin kan juna, da yin shawarwari da juna a Macao, don a daidaita sabanin da ake fuskanta ta hanyar yin shawarwari da juna, matakin da zai haifar da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankalin al'umma.

Daga karshe, Xi Jinping ya jaddada cewa,

"Abin da zan jaddada shi ne, bayan da kasar Sin ta maido da ikonta a yankunan musamman na Hong Kong da Macao, gudanar da harkokin yankunan harkokin cikin gida ne na kasar Sin, kuma ba za a yarda da sassan waje su tsoma baki a cikinsu ba. Gwamnatin kasar Sin da jama'ar ta, na da niyyar kiyaye ikon kasar, da tsaronta da ma muradunta, kuma ko kadan ba za mu yarda da sassan waje su tsoma baki cikin harkokin Hong Kong da na Macao ba." (Lubabatu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China