Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kauyen Shibadong a lardin Hunan na kokarin fita daga kangin talauci
2019-12-26 13:41:30        cri

Shekarar 2020, shekara ce da kasar Sin ke fatan samar da al'umma mai matsakaicin karfi daga dukkan fannoni. Samun nasarar yaki da kangin talauci, muhimmin aiki ne da ke gaba da komai, yayin da kasar Sin ke kokarin raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi.

A kwanakin baya, kasar Sin ta kaddamar da kan sarki guda 6, na tunawa da aikin yaki da talauci. Shin ko wadanne manyan nasarorin da aka samu a yankunan karkara, inda aka yi zane-zane kan wadannan kan sarki? Kuma mene ne ra'ayoyin wadanda suke zaune a wadannan yankunan karkara? Yau za mu ziyarci kauyen Shibadong da ke lardin Hunan, wanda ya samu babban ci gaba.

A cikin wadannan kan sarki guda 6 na tunawa da aikin yaki da talauci, akwai wani dangane da kauyen Shibadong, a gundumar Huayuan da ke lardin Hunan na kasar Sin, inda aka yi zane-zane kan sabuwar surar kauyen, sakamakon aiwatar da manufar yaki da talauci.

A kauyen Shibadong a gundumar Huayuan da ke yankin Xiangxi, matsakaicin fadin gonaki na ko wane mutum bai wuce murabba'in mita 670 kacal ba. Babu masana'antu a wurin. Yawancin mazauna wurin, 'yan kabilar Miao ne, wadanda ke fama da talauci. Sakamakon aiwatar da manufar yaki da talauci, ya sa kauyen Shibadong ya rubanya kokarin raya aikin yawon shakatawa a yankunan karkara, da ayyukan noman 'ya'yan itatuwan Kiwi, da fasahar yin amfani da allura da zare domin yin ado kan kyalle, ta hanyar dinki irin na kabilar Miao gwargwardon karfinsa. Sannu a hankali zaman rayuwar mazauna wurin na kyautatuwa.

Yang Bin mai shekaru 30 da haihuwa, ya taba yin aiki a ketare. Ya koma gida don ganin ci gaban da aka samu a garinsa. Yang Bin ya ce, yanzu yawancin matasa maza sun samu nasarar fita daga kangin talauci da kuma yin aure. Karfinsu na samun wadata ya kyautata sosai. "Yanzu 'yan kauyenmu suna da budaddiyar zuciya. A baya, suna jira a taimake su, suna dogaro da taimako, kuma su kan roki tallafin gwamnati. Amma yanzu ba su yin haka. Sun kyautata tunaninsu sosai. Sun yi kokari da kansu."

Kafin a ba da taimako wajen yaki da talauci, sai an kyautata halayyar mutane tukuna. Sakamakon daukar sabbin matakan kyautata halayyar mutane, alal misali, ba da ilmi kan kyautata da'a, da yin gasar raye-raye da wake-wake, da yin wasa da kalangu irin na kabilar Miao, da kuma samar da abin koyi wadanda suke zaune a wurin, a hankali a hankali ya sa tunanin mazaunan kauyen Shibadong ya kyautata, ba sa ci gaba da jira a taimake su, ba sa son dogaro da taimako, ko rokon tallafawar gwamnatin, domin kyautatuwar hallayar karfafa raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi. Yanzu 'yan kauyen Shibadong suna sayar da 'ya'yan itatuwansu na Kiwi, zuwa yankunan musamman na Hong Kong da Macao kai tsaye, wanda ribar da suka samu a shekarar 2017, ta kai kudin Sin RMB yuan dubu 740. A shekarar 2018 kuma, matsakaicin kudin shiga na ko wane mutum ya wuce yuan dubu 12 a kauyen na Shibadong. Sun Zhongyuan, sakataren sashen kauyen Shibadong na JKS ne, ya kuma yi karin bayani da cewa,"Mutene 533 daga iyalai 136 a kauyenmu na Shibadong sun fita daga talauci. Yawan masu fama da talauci ya ragu zuwa kaso 1.17 a kauyenmu, a maimakon kaso 56 a shekarar 2013. Kyautatuwar hallaya ta karfafa karfin fama da talauci. Yanzu mazauna kauyenmu na da karfin samun wadata, suna alla-alla wajen samun wadata, sa'an nan suna rubanya kokarinsu na samun wadata."

Baya ga kauyen Shibadong, mahukuntan yankin Xiangxi sun gabatar da yadda kauyen Changpu a gundumar Fenghuang, kauyen Hangka, kauyen Songjiazhai a gundumar Luxi da dai makamantansu, sun fitar da kansu daga kangin talauci. Sun kuma rika inganta ba da horo ta fuskar fasaha da sana'a, a kokarin kyautata karfin mazauna wurin na samun ci gaba da kansu. Ye Hongzhuan, sakataren kwamitin yankin Xiangxi na JKS ya nuna cewa, ya zama dole ne a taimaka wa masu fama da talauci dake son su fita daga talauci, kar su ji tsoron komai, kuma su samu dabarar fita daga talauci. "Muna tsayawa kan daukar hakikanin matakai, na sa kaimi kan masu fama da talauci, mu ba su jagora, kuma mu karfafa gwiwarsu wajen fita daga kangin talauci."

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China