Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Karatu a kasar Sin: dama ce mai samar da kalubale
2020-01-03 09:23:05        cri

 

 

 


Ofishin jakadancin Sin dake kasar Ghana, ya ce 'yan kasar ta Ghana 828 ne suka ci gajiyar samun horo da sanin makamar aiki a sassa daban daban, karkashin tallafin da Sin ke daukar nauyi cikin shekarar 2019.

Wata sanarwar da ofishin ya fitar ta nuna cewa, sassan da mutanen suka ci gajiyar samar da horon na Sin, sun hada da na rage talauci, da kiwon lafiya. Kana daga shekarar 2008 zuwa ta 2019, sama da 'yan Ghana 7,100 ne aka gayyata kasar Sin, domin halartar horo, da tarukan karawa juna sani daban daban.

Wannan wani misali ne ga huldar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da kasashen Afirka. Hakika dalibai 'yan Afirka da suke zuwa kasar Sin domin karatu na ta karuwa.

Wani rahoton da ma'aikatar aikin ilimi ta kasar Sin ta gabatar ya nuna cewa, yawan dalibai 'yan kasashen Afirka dake karatu a kasar Sin ya karu daga kusan dubu 2 na shekarar 2003 zuwa kimanin dubu 62 a shekarar 2016, inda adadin ya ninka har sau 31.(Bello Wang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China