Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Duniya na sa ran ganin karin gudummawar da kasar Sin za ta bayar a shekara ta 2020
2020-01-06 13:33:11        cri

Sabuwar shekarar da muke ciki, wato 2020, shekara ce mai ma'ana ta musamman ga kasar Sin, inda za ta cimma muradunta na raya zaman al'umma mai matsakaicin karfi da kammala samar da al'umma mai matsakaicin ci gaba ta kowace fuska, ya zuwa lokacin da jam'iyyar kwaminis ta kasar za ta yi bikin cika shekaru dari a shekara ta 2021.

A shekara ta 2020, kasashen duniya na sa ran ganin kasar Sin ta kara taka muhimmiyar rawa don kare ra'ayin kasancewar bangarori daban-daban ta hanyar fadada hadin-gwiwar kasa da kasa, da bullo da sabbin dabarun inganta harkokin mulkin duniya, gami da samar da sabon kuzari ga ci gaban kasa da kasa.

A shekara ta 2019, duniya na kara fuskantar kalubaloli a fannoin da suka shafi nuna bangaranci da ra'ayin bada kariya da kabilanci da sauransu, har ma akwai wasu kasashen da suka ci gaba da nuna babakere da mulkin danniya kan sauran kasashe.

A irin wannan halin da ake ciki, kasar Sin ta jaddada cewa ya kamata kasa da kasa su yi shawarwari kan batutuwan duniya don cimma matsaya daya.

A nasa bangaren, wani masanin dangantakar kasa da kasa na kasar Girka mai suna Vassiliki Souladaki, ya ce yana fatan ganin kasar Sin za ta kara bada gudummawarta ga ci gaban tattalin arzikin duniya mai dorewa, da taimakawa ga kafa wani tsarin kasa da kasa mai adalci da demokuradiyya wanda Majalisar Dinkin Duniya za ta zama jigonsa.

A shekara ta 2020 kuma, akwai kasashe da dama wadanda ke son zurfafa dangantakar abokantaka tare da kasar Sin, a wani kokari na kara samar da zaman karko da wadata da ci gaba ga duniya. A nasa bangaren, Roderich Ptak, wani shehun malami mai nazarin ilimin kasar Sin a kasar Jamus ya ce, kasarsa da kasar Sin dukkansu na kokarin yaki da ra'ayin bada kariya ga harkokin kasuwanci. Don haka yana matukar fatan kasashen biyu za su goyawa juna baya da samun fahimtar juna don sanya sabon kuzari ga duk fadin duniya baki daya.

A bana ake cika shekaru 75 da kafa Majalisar Dinkin Duniya, wadda tun farkon kafuwarta, ya zuwa yanzu, take nuna himma da kwazo wajen shimfida zaman lafiya da tabbatar da kwanciyar hankali gami da neman ci gaba a duniya.

A yayin da duniya ke kara fuskantar kalubale da matsaloli a 'yan shekarun nan, kasar Sin ta dade tana kare matsayin jigon MDD a harkokin duniya, da nuna azama wajen taimakawa ga tabbatar da cimma ajandar ci gaba mai dorewa na MDD zuwa shekara ta 2030, da halartar hadin-gwiwar kasa da kasa ta fannin shawo kan matsalar sauyin yanayi, tare kuma da bullo da dabarunta wajen yaki da ta'addanci a duniya.

A nasa bangaren, Vassiliki Souladaki daga kasar Girka na ganin cewa, sauyawar yanayi da matsalar ta'addanci da takarar da ake yi a fannonin makamashi da albarkatu da abinci da fasahohin halittu duk sun sa kasashe daban-daban na kara fuskantar sabbin kalubaloli. Ya ce yana fatan kasar Sin za ta taimaka ga kyautata tsare-tsaren duk duniya.

A nata bangaren, wata marubuciya 'yar kasar Faransa, kana masaniyar harkokin kasar Sin, Sonia Bressler ta bayyana cewa, kasar Sin ta samu ci gaba yadda ya kamata a karkashin yanayin sarkakkiya da duniya take ciki, kuma manufofin kasar za su ci gaba da taka rawar gani a tsarin siyasa da tattalin arzikin duniya.

Bugu da kari, a halin yanzu kasashen duniya na kara fuskantar matsalar rashin daidaiton ci gaba tsakaninsu. Ana ganin cewa, ya kamata a inganta hadin-gwiwar kasa da kasa don neman ci gaba tare. Wata muhimmiyar shawarar da kasar Sin ta fitar da ita, wato "ziri daya da hanya daya" za ta taimaka sosai ga raya kyakkyawar makomar bil'adama ta bai daya a duniya.

Tsohon babban mashawarci a tarayyar Afirka AU, wanda kuma shehun malami ne a jami'ar Addis Ababa dake kasar Habasha Costantinos Bt. Costantinos ya bayyana cewa, a shekara ta 2020, yana fatan ganin kasar Sin za ta ci gaba da aiwatar da ayyukan shawarar "ziri daya da hanya daya" ta yadda kasashen Afirka za su kara cin gajiya.

Har wa yau, an kafa babban yankin gudanar da kasuwanci maras shinge a nahiyar Afirka a shekara ta 2019, inda ake sa ran kafa wata babbar kasuwa dake shafar al'ummar da yawansu ya kai biliyan 1.2. Ismael Buchanan, babban malami dake koyar da ilimin siyasa a jami'ar Rwanda ya ce, yana fatan kasar Sin da kasashen Afirka za su ci gaba da fadada hadin-gwiwa a bangarorin da suka shafi zuba jari da kasuwanci da tsaro da muhimman ababen more rayuwar al'umma.(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China