Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Geng Shuang: Sukar shawarar ziri daya da hanya daya bai taba dakile hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar ba
2020-01-13 20:36:43        cri
Yanzu haka dan majalissar gudanarwar kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ke gudanar da ziyara a nahiyar Afirka tare yin musayar ra'ayoyi tare da shugabannin kasashen Afirka a kan shawarar "ziri daya da hanya daya". Kafin wannan kuma, wasu 'yan siyasa na yammacin duniya, na sukar manufar kasar Sin game da Afirka, inda suke cewa Sin na amfani da shawarar "ziri daya da hanya daya " ne, domin jefa kasashen Afirkan cikin tarkon bashi.

Game da hakan, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Geng Shuang, ya ce ba wata kasa a duniya da ta fada tarkon bashi, sakamakon jarin da Sin ta zuba mata.

Geng Shuang ya kara da cewa, "A iya sani na, ba wata kasa da ta tsunduma a tarkon bashi saboda jarin da kasar Sin ta zuba mata, kuma suka, ko kushe ga shawarar "Ziri daya da hanya daya " da wasu sassa ke yi, ba zai taba dakile ci gaban hadin gwiwar bangarorin kasa da kasa a fannin aiwatar da shawarar ba".

Kakakin ya kara da cewa, tuni aka sanya hannu kan takardu 199 tare da kasashe 137, da hukumomin kasa da kasa 30, ciki hadda kasashen Afirka 44, da wasu kwamitocin kungiyar AU, game da hadin gwiwar raya ayyukan dake kunshe cikin shawarar "ziri daya da hanya daya ". Hakan a cewar jami'in, shaida ce dake tabbatarwa duniya irin imani da kasashen duniya ciki hadda na Afirka suka yi, da kyawawan manufofin shawarar ta "Ziri daya da hanya daya ". Kaza lika hakan tamkar martani ne, ga masu zargi, ko kushe wannan shawara mai cike da fa'ida.

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China