Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Vladimir Putin ya nada Mikhail Mishustin a matsayin sabon firaministan kasar Rasha
2020-01-16 10:26:49        cri

Kafar yada labarai ta kasar Rasha ta ba da labari a jiya Laraba cewa, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya amince da rokon yin murabus da ministocin gwamnatin kasar da Dmitry Medvedev ya gabatar masa, inda ya gabatarwa majalisar wakilan kasar sunan Mikhail Mishustin, shugaban hukumar haraji, don nada shi sabon firaministan.

A wannan rana da safe, Dmitry Medvedev ya gabatar da rokon yin murabus din ministocin gwamnatinsa gaba daya. Daga bisani, Putin ya sa hannu kan umurnin shugaba na yarda da wannan roko, kuma ya yanke shawarar cewa, Dmitry Medvedev ya zama mukaddashin firaministan, kuma ya bukaci ministocin da suka yi murabus da su ci gaba da sauke nauyin dake bisa wuyansu kafin a kafa sabuwar gwamnati. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China