Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Turkiyya ta fara tura sojoji zuwa kasar Libya
2020-01-16 20:42:45        cri
Shugaba Recep Tayyip Erdogan na Turkiyya, ya ce kasar sa ta fara tura dakarun ta zuwa Libya, domin tallafawa rundunar sojin gwamanatin kasar mai samun goyon bayan MDD, dake da helkwata a Tripoli.

Shugaba Erdogan, wanda ya bayyana hakan yayin wani taron tantance ayyuka na 2019, wanda ya gudana a birnin Ankara a jiya Alhamis, ya ce "za mu aike da dakaru domin kiyaye halastacciyar gwamnatin kasar.

Shugaban na Turkiyya ya kara da cewa, kasar sa za fara gudanar da bincike da hako danyen mai, a yankin gabashin tekun Mediterranean, a sassan filayen da suka yi yarjejeniyar hakan da gwamnatin Libya mai helkwata a Tripoli. (Saminu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China