Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Kudancin Afrika na fuskantar matsananciyar yunwa sakamakon sauyin yanayi
2020-01-17 10:06:36        cri
Shirin samar da abinci na MDD (WFP) ya gabatar da bukatar neman taimakon kudaden da za'a gudanar da shirin yaki da matsalar yunwa a kudancin Afrika inda wasu al'umma masu yawa ke fuskantar matsanancin karancin abinci wanda sauyin yanayi da durkushewar tattalin arziki suke haddasa a yankin.

An yi kiyasin mutane miliyan 45 daga cikin mutane miliyan 345 a yankin hamada musamman mata da kananan yara suna fama da matsalar karancin abinci sakamakon mummunan fari, gami da ibtila'in ambaliyar ruwa, da tabarbarewar tattalin arziki dake addamar shiyyar, daraktan shirin WFP a kudancin Afrika Lola Castro shi ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa.

Casro ya ce akwai bukatar kasa da kasa su kara kaimi don samar da tallafin gaggawa ga miliyoyin jama'a a shiyyar kudancin Afrika, da kuma zuba jarin dogon lokaci wanda zai taimakawa mutane marasa galihu a shiyyar wajen jure matsanancin sauyin yanayin dake kara ta'azzara a yankin.

WFP yana shirin samar da taimako ga mutane miliyan 8.3 da matsalar ta shafa ko kuma suke cikin bukatar taimakon gaggawa saboda matsananciyar yunwa a kasashe 8 da matsalar tafi kamari da suka hada da Zimbabwe, Zambia, Mozambique, Madagascar, Namibia, Lesotho, Eswatini da Malawi. (Ahmad Fagam)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China