Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
MDD: Tattalin arzikin duniya yana iya bunkasa da kaso 2.5 a shekarar 2020
2020-01-17 10:13:54        cri
Wani rahoto da MDD ta fitar kan yanayi da makomar tattalin arzikin duniya (WESP) a shekarar 2020, ya nuna cewa, akwai yiwuwar tattalin arzikin duniya zai bunkasa da kaso 2.5 cikin 100 a wannan shekara, amma fa, tankiyar cinikayya da rikicin kudi ko karuwar zaman dar-dar a harkokin siyasar duniya, na iya mayar da hannu agogo baya.

Rahoton wanda aka kaddamar jiya Alhamis a hedkwtar MDD dake birnin New York, ya nuna yadda bunkasar tattalin arzikin za ta ragu da kaso 1.8 cikin 100 a wannan shekara. Haka kuma tafiyar hawainiya kan ayyukan tattalin arzikin na dogon lokaci, shi ma yana iya haifar da koma baya a fannin ci gaban mai dorewa, ciki har da manufofin kawar da talauci da samar da ayyukan yi masu kyau ga kowa.

Rahoton ya kara da cewa, rashin daidato da karuwar matsalar sauyin yanayi, suna kara haifar da matsaloli a sassa da dama na duniya. (Ibrahim Yaya)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China