Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Xi Jinping ya halarci jerin bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Myanmar tare da kaddamar da shekarar yawon shakatawa tsakanin kasashen biyu
2020-01-18 11:09:21        cri

Da yammacin jiya Jumma'a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya halarci jerin bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Myanmar tare da kaddamar da shekarar yawon shakatawa tsakanin kasashen biyu a birnin Naypyidaw, fadar mulkin Myanmar, inda ya ce, shi da takwaransa na Myanmar sun cimma matsaya daya kan hada kan kasashensu don gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya.

Shugaba Xi Jinping ya mika gaisuwarsa da yaren Myanmar don fara gabatar da jawabinsa a wajen bikin kaddamar da jerin bukukuwan murnar cika shekaru 70 da kulla huldar diflomasiyya tsakanin Sin da Myanmar da shekarar yawon shakatawa ta kasashen biyu.

Shugaban kasar Myanmar Win Myint da shugabar gwamnatin kasar Aung San Suu Kyi da sauran wasu manyan jami'an gwamnatin kasar sun halarci bikin.

Xi ya ce, al'ummar Sin da Myanmar na yaukaka dadadden zumuncin dake tsakaninsu, kuma suna da kyakkyawar al'ada da ingantaccen tushe na fahimtar juna da taimakawa juna, inda ya jaddada cewa:

"Kasashen biyu na makwabtaka da juna, kuma al'ummarsu na da dadadden zumunci har ma al'adunsu akwai kamanceceniya da dama. Irin 'yan uwantaka tsakanin Sin da Myanmar na tsawon shekara da shekaru na taimakawa sosai ga ci gaban dangantakar kasashen biyu. Ya kamata bangarorin biyu su kara samun fahimtar juna ta fannin wayar da kan juna da inganta mu'amala tsakanin al'ummarsu domin kara karfafa dankon zumunci tsakaninsu."

Shugaba Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, akwai muhimmancin gaske wajen ci gaba da raya huldar kasashen biyu a sabon zamanin da muke ciki, kuma shugabannin biyu sun cimma maslaha na gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya, domin kafa sabuwar alkibla ga bunkasuwar dangantakar kasashe biyu a nan gaba. Shugaba Xi ya ce:

"Ni da takwarana na Myanmar wato Win Myint mun amince da gina al'umma mai kyakkyawar makoma ta bai daya tsakanin kasashenmu, al'amarin da ya shaida irin kyakkyawar dangantaka ta dogaro da juna da taimakawa juna tsakaninmu."

Har wa yau, shugaba Xi ya jaddada cewa, ya kamata kasashen biyu su fadada hadin-gwiwarsu ta kawowa juna moriya, ta yadda al'ummarsu za su kasance makwabta da aminai da kuma 'yan uwa na kwarai har abada.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Myanmar Win Myint ya bayyana cewa:

"A yayin da ake cika shekaru 70 da kafa huldar jakadanci tsakanin Sin da Myanmar, shugaba Xi Jinping ya kawo ziyarar aiki a Myanmar domin taya murnar wannan muhimmin lokaci tare da mu, al'amarin da ya shaida dadadden zumunci tsakanin kasashen biyu da al'ummarmu baki daya. Kasar Myanmar za ta ci gaba da dukufa wajen habaka hadin-gwiwa tare da kasar Sin a bangarori daban-daban. Allah yar karfafa zumunci tsakanin Sin da Myanmar!"(Murtala Zhang)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China