Facebook Twitter
in Web hausa.cri.cn
Ziyarar Xi ta bude sabon shafi na hadin kai da sada zumuncin Sin da Myanmar
2020-01-19 15:14:11        cri

Jiya Asaba shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kammala ziyarar aikinsa a Myanmar. Yayin ziyara ta kwanaki biyu, shugaba Xi ya halarci ayyuka 12, tare da sanya ido kan takardun kulla yarjejeniyar hadin kai tsakanin kasashen biyu kimanin 29. Bangarorin biyu na kai ga matsaya daya na raya kyakkyawar makoma mai haske na al'umomin biyu baki daya, da kuma bayar da wata hadaddiyar sanarwa cikin hadin gwiwa don tsai da tsare-tsaren da bangarorin biyu za su yi na tuntubar juna da hadin kai a sabon zagaye, matakin da ya bude sabon shafi na hadin kai da sada zumuncin Sin da Myanmar.

Ban da wannan kuma, shugabannin kasashen biyu sun yi musayar ra'ayi kan yadda za a kara dakon zumuncinsu da ingiza hadin kai bisa manyan tsare-tsare a dukkan fannoni da raya kyakkyawar makoma mai haske ga al'umomin kasashen biyu baki daya, tare da cimma matsaya daya, matakin da ya samar da yanayi mai kyau ga bunkasuwar dangantakar kasashen biyu a sabon zamani. Shugabar gwamnatin kasar Myanmar, Madam Aung San Suu Kyi ta yi tsokaci cewa, ziyarar Xi Jinping a wannan karo tana da ma'ana matuka, wadda ta zurfafa zumuncin jama'ar kasashen biyu kuma za ta ingiza hadin kan kasashen biyu.

An ce, ziyarar aiki da shugaba Xi Jinping ya yi a wannan karo a Myanmar, sabuwar dan ba ce a cikin tarihin dangantakar kasashen biyu, wadda za ta haifar da sakamako mai yakini wanda zai amfanawa kasahen biyu da sa kaimi ga bunkasuwar wannan yanki har ma ga wadatar duniya baki daya. (Amina Xu)

 

Labarai masu Nasaba

 

 

 

 

Mafiya Karbuwa

 

 

 

 

® China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China